Tsohon mai taimakawa Buhari kan sabbin kafafen yaɗa labarai Bashir Ahmad ya zargi abokin ɗan takarar sa Mahmud Gaya da murɗe zaɓen fidda gwani da aka yi ranar Alhamis a Kano.
A doguwar jawabi da ya saka a shafinsa ta Facebook, bashi ya ce an yi masa karfa karfa ne a wajen zaɓen fidda gwanin.
” Abin mamaki a ce wai ni kai na da zo wurin zaɓen da kyar aka bari na shiga zauren da ka gudanar da zaɓen. Ƴan daba ne kawai suka zagaye wurin duk sun hana deliget shiga.
” Na fito takara ne domin in wakilci mutane na amma ba wai don wata manufa ba. Ko da na shiga zaurin taron kuma na ga abinda ake yi ba irin abinda ya kamata ba ne sai na na fice daga ciki.
Bashir ya yi kira ga jam’iyyar da madu faɗa a APC da su gaggauta soke wannan zaɓe, sannan a sake shirya wani zaɓen tunda wuri.
” Yin haka shine zai karawa jam’iyyar mu ta APC daraja sannan ya ceto ta daga masu ƙarfa ƙarfa a jam’iyyar.
” Ni dai Bashir Ahmad ban amince da sakamakon zaɓen ba kuma ina kira da a gaggauta sake zaɓen domin ceto jam’iyyar daga hannun miyagun ƴan siyasa.
Mahmud Gaya wanda shine ɗan majalisan da ke kan kujera ya lashe zaɓen da ƙuri’u 198 inda shi kuma Bashir ya samu kuri’u 16 kacal.