Daya daga cikin ƴan takarar gwamnan jihar Cross Rivers Wilfred Bonse karkashin jam’iyyar PDP ya rubuta wa uwar jam’iyyar PDP wasikar neman jam’iyyar ta biya kuɗin fom din rakarar gwamna da ya siya.
Bonse ya ce tunda an ki bashi dama ya bayyana a gaban kwamitin tantance ƴan takarar gwamna na jam’iyyar a biya shi kuɗin fom din sa.
” A biya ni naira miliyan 21 kuɗin fom ɗin takarar gwamna da na siya tun da wuri. Ba cika dukka sharuɗɗan da jam’iyyar ta gindaya domin tantance ɗan takara amma aka yi kumbiya-kumbiyar da dole aka hana ni takara
” Tun da an hana ni takara, ai sai abiya ni kuɗin fom ɗina domin na rubuta wa shugaban jam’iyyar PDP a can Abuja kuma na samu tabbacin ya samu wasika ta.
Bonse ya kara da cewa ya gama shawarar canja sheka zuwa wata jam’iyyar nan ba da daɗewa ba.
” Ni fa na gama shawara zan koma wata jam’iyyar. Na lura cewa tsorona suke yi kada in kawo musu cikas a zaben da ke tafe saboda fice da nayi a siyasar jihar da kuma dandazon magoya baya da nake da su.
” Babu abinda ba a ce in kawo ba a lokacin zaman kwamitin tantance ƴan takara kuma babu wanda ban kawo amma duk da haka sai da aka nuna min rashin mutunci, toh nima sai an biya kuɗin fom ɗina, naira miliyan 21 cas.