Hukumar EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, ana cajin sa da wawurar Naira biliyan 2.9 a lokacin da ya ke Gwamnan Jihar Imo.
EFCC ta gurfanar da shi a ranar Litinin, tare da wani mutum mai Anyim Nyerere, wanda ake tuhumar su tare
An gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo, yayin da lauyan EFCC Gbolahan Lotana ya nemi alƙali ya sa ranar da zai fara shari’ar.
Sai dai kuma lauyan Okorocha, Okey Amaechi (SAN) ya roƙi a ba shi belin Okorocha. Ya kuma ce ci gaba da tsare Okorocha zai kawo masa naƙasu sosai wajen takarar shugabancin ƙasa da ya fito takara, kuma a ƙarshen makon nan za a yi zaɓen fidda gwani na APC ɗin.
Mai Shari’a ya ce sai washegari a 31 Ga Mayu za a duba yiwuwar bayar da beli.
EFCC ta kama Okorocha bayan ya shafe watanni fiye da huɗu ya na zillewa daga kin karɓar sammaci.
Ana tuhumar Okorocha da laifuka 17 da yawancin su duk na zambar maƙudan kuɗaɗe ne.
Premium Times Hausa ta bada labarin yadda Minista Malami ya nemi hana EFCC kama Rochas Okorocha.
Minista Abubakar Malami wanda kuma shi ne Antoni Janar Mai Kula da Ƙararraki baƙi ɗaya, ya yi ƙoƙarin hana Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa kama tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, amma Bawa ya ƙi bin umarnin sa.
Wasu takardun bayanai daga su ka faɗo hannun PREMIUM TIMES, ita kuma ta damƙe, sun tabbar da cewa Minista Malami ya rubuta wa Bawa wasiƙa a ranar 21 Ga Afrilu, inda ya umarce shi da ya daina binciken Rochas Okorocha kawai.
Malami ya aika wa EFCC da wasiƙar a daina binciken Rochas Okorocha, wanda Sanata ne na APC a yanzu haka, bayan da lauyan Okorocha ɗin Ola Olanipekun ya rubuta wa Malami takardar ƙorafi kan EFCC.
Takardar da lauyan Okorocha ya rubuta wa Malami, ta na ƙunshe da zargin EFCC ta take umarnin Babbar Kotun Tarayya ta Fatakwal, wadda ta yanke hukuncin cewa kwamitin binciken da aka kafa wa Okorocha ya hana shi haƙƙin sa na ba shi damar kare kan sa da yi masa adalci. Kuma kwamitin ya nuna kamar Okorocha ya ma aikata laifin tun kafin kotu ta tabbatar da aikatawar a kan sa.
Malami ya yi wa EFCC nuni da Sashe na 6(6) na Kundin Mulkin 1999, bisa hukuncin da Babbar Kotun Fatakwal ta yanke, a ƙara mai lamba FHC/ABJ/C5/45/2019.
Sai dai kuma EFCC ta yi watsi da umarnin Malami, inda kwanan baya ta yi masa dirar-mikiya a gida, a Abuja.
Okorocha ya ƙi fitowa, inda EFCC ta kewaye gidan tsawon sa’o’i shida. A ƙarshe dai su ka fara rufin gidan su ka kama shi, su ka tafi da shi.
EFCC ta ce Okorocha ya karya ƙa’idar belin kan sa da ta bayar, domin ya karya belin da ta ba shi.
Sannan kuma akwai takardun kotu da ya ƙi yarda ya karɓa matsayin sammaci, dangane da shari’ar zargin danne naira biliyan 2.9 da ake yi masa.
Discussion about this post