Bisa ga alkaluman da aka fitar ya nuna cewa an samu raguwa a yawan mutanen da ‘yan bindiga suka kashe a wannan makon.
Ƴan bindigan sun kashe wata dalibar kwaleji a jihar Sokoto saboda fadin kalamun batanci ga Annabi da ta yi a jihar.
Sannan Boko Haram sun kashe Sojoji a jihar Taraba.
Mafi yawan mutanen da ‘yan bindiga suka kashe sun kashe su ne a yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma.
PREMIUM TIMES ta rawaito haka daga rahotannin da jaridu suka buga a makon jiya.
Arewa maso Yamma
A ranar Lahadin da ya gabata ne ‘yan bindiga suka kashe mutum bakwai a karamar hukumar Maradun dake jihar Zamfara.
Majiya daga kauyen sun bayyana cewa maharan sun kashe wadannan mutane a kauyukan Faru da Kauyen Minane.
A ranar Lahadin ne kuma ‘yan bindigan suka kashe mutum uku sannan wasu mutum uku sun ji rauni a kauyen Gurbin Magarya dake karamar hukumar Jibia.
Maharan sun afka kauyen da misalin karfe 10 na dare sannan sun kashe dabobbin mutanen kauyen da dama.
A jihar Kaduna ‘yan bindiga sun kashe limamin cocin Katolika na St John Joseph Akete dake kauyen Kudenda a karamar hukumar Chikun.
Shugaban cocin Christian Emmanuel ya sanar da haka ranar Laraba.
A ranar Alhamis ne daliban kwalejin ilimi na Shehu Shagari a jihar Sokoto sun kashe wata dalibar kwalejin Deborah don ta fadi kalaman batanci ga Annabi Muhammed (SAW).
Daliban sun yi wa Debora ruwan duwatsu kuma sun lakada mata dukan tsiya sannan suka kona ta.
A dalilin haka ne hukumar makarantar ta rufe makarantar har sai illa mashaAllahu.
Arewa maso Gabas
‘Yan bindiga sun kashe Sojoji shida a kauyen Tati dake karamar hukumar Takum a jihar Taraba
Maharan Wanda suka afka kauyen da misalin karfe 10 na dare sun yi bata kashi da sojojin bataliya 93.
Bayan haka kwamandan sojojin bataliya 93 ya bace bayan kungiyar ISWAP sun dana tarko wa sojojin a jihar.
Daga nan a jihar Bauchi ‘yan bindiga sun kashe mutum uku sannan mutum daya ya ji rauni a kauyukan Yadagungume da Limi dake karamar hukumar Ningi ranar Laraban da ya gabata.
Shuaibu Salihu mai shekara 17, Ruwa Ali Wanda aka fi sani da Mai Inji mai shekara 45 da Sunusi Burra na daga cikin mutanen da maharan suka kashe
Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum uku a kauyen Num dake karamar hukumar Tafawa Balewa.
Kakakin rundunar Ahmed Wakil wanda ya tabbatar da haka ranar Alhamis ya ce mutum biyu sun ji rauni a dalilin harin.
Kudu maso Yamma
‘Yan bindiga sun yi wa ma’aikatan hukumar JAMB fashion da makami a otel din Mabila Hotel dake Ikorodu a jihar Legas a safin Laraban da ya gabata.
Maharan sun kashe mai gadin dake fadi a otel din.
Discussion about this post