Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ta ɗage ranar da za ta tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa, amma kuma ba ta faɗi wata ranar da za a yi tantancewar ba.
Cikin wata sanarwa da Kakakin APC Felix Morka ya fitar, ya ce an ɗage tantancewar wadda a baya aka shirya yi a ranar Litinin, 23 Ga Mayu.
APC ta ce babu wata ranar da aka aza domin yin tantancewar.
Ba wannan ne karo na farko ko na biyu da APC ta ɗage tantance ‘yan takarar ta ba.
Tun da farko an shirya yin tantancewar a ranakun 14 da 15 Ga Mayu, amma aka ɗage zuwa ranar 23 Ga Mayu.
Kwana ɗaya kafin ranar kuma sai ga sanarwa a ranar 22 Ga Mayu, mai ɗauke da sa hannun Felix Morka cewa, an ɗage tantancewar har sai yadda hali ya yi.
APC dai ta shirya gudanar da Taron Gangamin Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa a ranakun 29 da 30 Ga Mayu, 2022.
Amma jam’iyyar ta tantance ‘yan takarar sanatoci, na Majalisar Tarayya da sauran su.
Hukumar Zaɓe Ta Ƙasa INEC dai ta gargaɗi dukkan jam’iyyu cewa ba za a ƙara masu ko da wa’adin kwana ɗaya ba, daga wa’adin rufe karɓar sunayen ‘yan takara wanda Dokar Zaɓe ta Ƙasa ta gindiya ba.
Akwai masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC har mutum 25.
Kwan-gaba-kwan-bayan APC Wajen Canja Ranaku:
APC ta yi canja ranar zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa:
Jam’iyyar APC ta sauya ranakun da za ta gudanar da zaɓen fidda-gwanin ‘yan takarar zaɓukan 2023.
Cikin sabuwar tantebur ɗin da Sakataren APC na Ƙasa, Felix Morka ya sa wa hannu kuma ya fitar a ranar Laraba, ta nuna cewa Gangamin Taron Musamman domin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa zai gudana ne a ranakun 29 da kuma 30 Ga Mayu.
Idan ba a manta ba, a taron da Masu Ruwa da Tsaki na APC su ka yi a baya, sun tsayar da ranakun 30 Ga Mayu zuwa 1 Ga Yuni za a yi zaɓen fidda gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a APC.
Kwamitin Zartaswa na Masu Ruwa da Tsaki sun miƙa ragamar mulkin jam’iyya ga Kwamitin Dattawa na Shugabanni waɗanda za su ci gaba da riƙewa har bayan kammala zaɓen fidda-gwani.
Morka ya ce sabbin ranakun shirya zaɓen fidda-gwanin Gwamnoni, Sanatoci, Wakilan Tarayya da na Majalisar Dokokin Jihohi su ma an canja su.
A ranar 26 Ga Mayu ne za a yi zaɓen fidda gwani na Gwamnoni da ‘yan Majalisar Tarayya. Sai kuma washegari ranar 27 Ga Mayu a bada damar ɗaukaka ƙara idan akwai ƙorafe-ƙorafe dangane da zaɓen.
A ranar 27 Ga Mayu ce ranar zaɓen ‘yan takarar Sanata da Majalisun Jihohi. Sai kuma washegari 28 Ga Mayu wanda ke da ƙorafi.
Idan ba a manta ba, a baya an shirya yin zaɓen fidda gwani na Gwamnonin APC ne a ranar 20 Ga Mayu.
Morka dai bai bayar da dalilin canja ranakun ba.
Idan za a tuna, ita kuwa APC ta shirya na ta taron zaɓen fidda-gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa a ranar 28 da 29 Ga Mayu, a babban filin wasan Abuja.
Premium Times Hausa ta buga labarin cewa INEC ta ƙayyade wa jam’iyyu wa’adin kammala zaɓuɓɓukan fidda gwani.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyun siyasa da su tabbatar da cewa sun kiyaye jadawalin gudanar da zaɓuɓɓukan su na fidda gwani na manyan zaɓuɓɓukan shekarar 2023.
Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da kan Masu Zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bada wannan gargaɗin cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
Okoye ya tunatar da cewa a ranar 26 ga Fabrairu, 2022, hukumar ta fitar da Jadawali da Tsarin Ayyuka na Manyan Zaɓuɓɓukan 2023, inda ta tanadar wa jam’iyyun da cewar su gudanar da zaɓuɓɓukan fidda gwanayen su don tsaida ‘yan takara daga ranar 4 ga Afrilu zuwa 3 ga Yuni, 2022.
Wannan na nufin cewa hukumar ba za ta amince da duk wani zaɓen fidda gwani da aka yi bayan wa’adin ya cika ba.
Kwamishinan ya ce: “Domin kiyaye sashe na 82(1) na Dokar Zaɓe ta 2022, dukkan jam’iyyun siyasa 18 sun bada sanarwar da ake buƙata da ke nuna ranakun da za su yi manyan tarurrukan su na ƙasa, da zaɓuɓɓukan fidda gwani domin tsayar da ‘yan takarar muƙamai daban-daban kamar yadda aka zayyana a Tsarin Mulki da Dokar Zaɓe.
“Wasu daga cikin jam’iyyun har sun fara aikin, wanda ya sa hukumar ta tura ma’aikata domin su sa ido kan yadda ake ayyukan kamar yadda doka ta buƙace ta ta yi.
“Saboda ganin muhimmancin aikin wajen samar da ‘yan takarar muƙamai daban-daban na zaɓe a Manyan Zaɓuɓɓukan 2023, ya na da muhimmanci a tunatar da jam’iyyun siyasa cewa ya rage masu wata ɗaya daga yau su kammala zaɓuɓɓukan su na fidda gwani.
“Wa’adin ƙarshe dai shi ne ranar Juma’a, 3 ga Yuni, 2022. Yayin da ta ke kira ga jam’iyyun da su tabbatar da sun yi zaɓe babu wata hatsaniya, kuma fisabillahi, hukumar ta na nanata cewa wa’adin na nan daram daƙam babu canzawa.”
Okoye ya kuma ce ana so a miƙa sunayen ‘yan takarar zaɓen Shugaban Ƙasa da Majalisar Tarayya ne ta hanyar gidan yanar INEC daga ranar 10 zuwa 17 ga Yuni, yayin da za a miƙa sunayen ‘yan takarar gwamna da majalisun dokokin jihohi daga ranar 1 zuwa 15 ga Yuli.
“Ana ƙara tunatar da jam’iyyun siyasa cewa tilas ne sunayen ‘yan takarar da za su miƙa wa hukumar su kasance waɗanda aka samar ne ta hanyar zaɓen fidda gwani da aka yi fisabilillahi.”
Okoye ya ce hukumar za ta ci gaba da yin aiki tare da jam’iyyun siyasar don tabbatar da an kiyaye Tsarin Mulki da Dokar Zaɓe da jadawalin dukkan ayyukan da aka tsara yi a cikin Jadawali da Tsarin Ayyukan Manyan Zaɓuɓɓukan 2023.