Wasu daga cikin ƴan siyasan Najeriya sun yi dakon fastoci har kasar Saudiya, gaban Ka’aba domin yi wa gwanayen su kamfen a can kasar.
Wani masoyin ɗan takarar shugaban ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ya rika nuna fastan Tinubu a wajen ɗawafi a ka’aba.
A wani hoto da ya karaɗe shafukan yanar gizo, wasu larabawa da ke ɗawafi a ka’aaba suna ta kallon wannan bawan Allah.
Idan ba a manta ba, a cigaba da shirin fafatawa a takarar shugabancin ƙasar nan, masoya Tinubu sun gudanar da ɗawafi na musamman da yin rokon Allah, Allah ya ba shi nasara a zaben dake tafe.
An yi wa Tinubu Ɗawafi na Musamman a Ka’aba, don neman yin nasara a 2023
Ɗimbin ‘yan Najeriya sun hallara Makka, Saudi Arabiya domin gudanar da Ɗawafi na Musamman, neman nasara kan Bola Tinubu domin yin nasara a zaɓen fidda-gwanin APC da kuma nasarar zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Masu yin Ɗawafin za sun sanya farin harami, inda kafin su ƙarasa sai da duka suka hallara a ƙofar shiga Ka’aba mai suna Ƙofar Sarki Abdul’aziz.
Manyan malamai da manyan ‘yan siyasa daga Najeriya sun halarci ɗawafin, ciki har da Kakakin Majalisar Jihar Legas, Obasa, wanda shi ne ma ya ce kuma za su gode wa Allah (SWT) domin Tinubu ya yi nasara.
Obasa ya ce dukkan waɗanda su ka yi ɗawafin dai sun yi imani da Allah cewa Tinubu ne zai yi nasara.
“Mun zo ne domin mu nemi sa’a da biyan buƙatar ganin Tinubu ya yi nasara a zaɓen 2023 ” Inji Obasa.
“Muna neman biyan buƙatar Allah domin Tinubu ya yi nasara.
“Tunda mun san dai mun tuntuɓi dimbin mutane kuma mun yi shirin ganin nasara daga wurin Allah.”
Obasa ya roƙi sauran Musulmi da ke ɗawafin Umra su shiga cikin zugar su, domin a yi ɗawafin tare da su.