‘Yan bindigan da suka yi garkuwa da faston cocin Katolika dake jihar Akwa-Ibom sun bukaci a biya naira miliyan 100 kudin fansa.
Ƴan bindigan sun yi garkuwa da Alphonsus Uboh limamin cocin St Pius dake kauyen Ikot Abasi Akpan, a karamar hukumar Mkpat Enin ranar Lahadin da ya gabata da misalin karfe bakwai na yamma a cikin gidan sa dake cocin bayan mata sun kammala taron Lahadi na 2022.
Shugaban kwamitin gudanarwa na cocin Cletus Okodi ya ce ya yi magana da faston a wayar salula ranar Litini inda ya ce maharan sun tsare shi a wani daji sannan suna bukatar a biya Naira miliyan 100 kafin su sake shi.
Tsohon shugaban kungiyar matasa na cocin Uwemedimo Patrick ya ce ya yi magana da shi a wayar kafin aka kashe wayar gaba daya.
Kakakin cocin Justin Udoma Shima ya tabbatar da sace faston da aka yi sai dai ya ce babban faston cocin ne yake da ikon yin magana da manema labarai.
Yin garkuwa da Uboh shine karo na biyu da maharan ke yi a jihar a cikin makonni uku da suka wuce.
Masu garkuwa sun yi garkuwa da faston cocin Solid Rock John Okoriko makonin biyu da suka gabata.
Maharan sun bukaci a biya naira miliyan 100 kafin su sake shi shima
Zuwa yanzu babu wanda ke da tabbacin ko wadanda suka yi garkuwa da Okoriko sune suka yi garkuwa da Uboh.
Discussion about this post