Shugaban Kamfanin Yada Labarai na Qausain TV, Alhaji Nasir Musa Idris, wanda aka fi sani da Albanin Agege, ya ce sun zabi gidan Rediyon BBC Hausa ne domin kulla kawance saboda shahararsu da ingancinsu ta fuskar yada labarai a fadin duniya.
Shugaban ya bayyana haka ne a yayin wata hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa a lokacin da ya kai wata ziyarar aiki a sashen Hausa na BBC dake birnin Landon a Kasar Birtaniya karshen wannan makon.
Nasir Musa ya ce tashar tasu wadda ke kan tauraron Dan Adam na Eutelsat 16 A, ta zabi hadin gwiwa da BBC Hausa ne domin kara inganta shirye-shiryen su, wadda dama ya ce tuni al’umma ke dakon jiran tashar Qausain TV, sakamakon kyawawan shirye-shiryen da suka bambanta da sauran tasoshin TV a fadin Najeriya.
“Mun fara yada shirye-shiryen mu tun a ranar 1 ga Watan Oktobar 2021, wadanda suka hada da labarai, rahotanni, siyasa, nishadi, al’adu da addini da sauransu. Kuma babban abin sha’awa shine yadda muka dauki harsuna 3 domin kawata shirye-shiryenmu da su, inda muka baiwa harshen Hausa kashi 70, sannan turanci da larabci kaso 15 kowannensu,” inji shi.
Da aka tambaye shi game da kalubalen da tashar ke fuskanta, Nasir Musa Idris, ya bayyana rashin wutar lantarki da rashin karfin intanet da kuma karancin tallace-tallace a matsayin manyan kalubalen da tashar ke fuskanta.
Yana mai cewa kamfanin na kashe makudan kudade wajen gudanarwa, musamman dawainiyar man dizel da biyan albashi da sauransu. Amma ya ce kawo yanzu an fara sanin tashar, kuma suna fatan fara samun tallace-tallace domin samun damar yada manufofin da suka jima suna ciwa Arewa tuwo a kwarya.
Discussion about this post