Tun bayan zaɓin Nasiru Gawuna, wato mataimakinsa da Kwamishinan Kananan hukumomin jihar Sule Garo, wasu daga cikin ƴan takarar gwamnan jihar Kano suka yi wa gwamna Abdullahi Ganduje bore.
Ƴan takarar sun ce su ba su anince da zabin Gawuna da Ganduje yayi saboda haka da shi da ɗan takarar sa su yi shirin fafatawa da su a filin daga, wato a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Wasu da dama na ganin gwamna Ganduje ya saka wa Gawuna da Garo ne bisa nuna rashin mutuncin da suka yi wajen kekketa takardar shigar da sakamakon zaɓe da suka yi da ya kai zaɓen Kano ga ‘Inkonkulusib’, wanda dukkan sai da ƴan sanda suka yi awon gaba da su.
Sai dai kuma hakan da Ganduje yayi ya bai hana wasu ƴan takara cigaba da kamfen da neman kuri’un wakilan jam’iyyar domin yin nasara a zaɓen fidda gwani.
Inuwa Waya, ɗaya daga cikin ƴan takarar gwamnan jihar ya ce zaɓin Gawuna bai ɗaɗa shi da ƙasa ba ko kaɗan.
” Don Ganduje ya zaɓi Gawuna a matsayin khalifan sa, ba zai sa in ɗaga kafa daga takarar da nake yi ba. Za mu fafata a zabe
Haka nan shima tsohon shugaban majalisan jihar Kani, Kabiru Alhassan, shim ya ce da shi za a fafata. Shaaban Sharaɗa, ɗan majalisan tarayya shima ya ce bai amince da naɗin Gawuna da Ganduje yayi ba, za a fafata da shi.
Sai dai kuma sanata Barau Jibrin da ya fito takarar gwamna ya janye, ya siya fom ɗin takarar Sanata kujerar da yake akai.
Sanata Jibrin zai fafata da gwamna Ganduje wanda tuni shima ya sayi fom ɗin takarar Sanata zai fafata da Jibrin.
Discussion about this post