Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta bayyana cewa ta yi nasarar kashe wasu da ake zargi masu yin garkuwa da mutane ne uku bayan arangama da suke yi da su.
‘Yan sandan sun kuma kama mutum biyu sannan sun ceto wani mutum daya da aka yi garkuwa da shi.
Jami’an tsaron sun samu nasara a kan ƴan bindiga a dalilin haɗin kai da suka samu daga mafarautan yankin Fufure, kamar yadda Kakakin rundunar Suleiman Nguroji ya faɗi a garin Yola ranar a cikin makon jiya.
Nguroji ya ce jami’an tsaron sun yi arangama da maharan a ranar 17 ga Mayu a tsaunin Samlo dake kusa da garuruwan Chigari da Gurin.
“Ko da Maharan suka hango jami’an tsaro sun tunkaro su sai suka buɗe musu wuta, daga nan kuma sai Allah ya baiwa jami’an tsaro sa’a akan su suka kashe uku daga cikin su.
“Jami’an tsaron sun ceto mutum daya mai suna Buba Hamidu mazaunin kauyen Samlo dake karamar hukumar Fufore.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sikiru Akande ya yaba kokarin ‘yan sandan dake Chigari da mafarauta ke yi.
Ya yi kira ga sauran DPO dake jihar da su mike tsaye wajen yaki da mahara da sauran Bata gari a jihar.