Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke malamin makarantar firamare dake Ago Iwoye mai suna Ayobami Runsewe mai shekara 25 da laifin yi wa ɗalibar sa mai shekaru 13 fyade.
‘Yan sandan sun kama Runsewe ranar a cikin makon jiya bayan mahaifiyar yarinyar ta kai kara a ofishin ‘yan sanda dake Ago Iwoye.
Kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi wanda ya sanar da haka wa manema labarai ya ce Runsewa ya tilasta yarin sannan yayi lalata da ita a gidan sa.
Ya ce malamin ya yi lalata da yarinyar da misalin karfe 4:30 na yamma bayan an tashi makaranta.
Oyeyemi kara da cewa mahaifiyar ta kawo kara ofishin ‘yan sandan tare da ‘yar da jini a riganta.
Ya ce nan da nan DPO din ofishin ‘yan sandan dake Ago Iwoye, SP Noah Adekanye ya jarorancin ‘yan sanda su ga garzaya har gidan malamai suka kamo shi.
A hannun ‘yan sanda Runsewe ya musanta yin lalata da yarinyar amma da ya ga yarinyar a ofishin ‘yan sandan sai ya yi shuru ya gagara magana.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Lanre Bankole ya ce fannin gurfanar da masu aikata laifi irin haka na jihar za ta ci gaba da bincike akai sannnan duk wanda aka kama da laifi zai ɗandana kudar sa.