” Badun Allah ya sa an jibge jami’an tsaro da ƴan banga a kusa da hanyar shiga garin Gurbin Magarya ba da gaba ɗaya kaf, ƴan bindigan sun gama da garin.” In ji Halliru Halidu.
Ƴan Bindiga sun kai farmaki garin Gurbin Magarya da misalin karfe 10 na dare inda suka daddatse hanyoyin shiga garin.
Haladu ya ce waɗanda suka rasu sun haɗa da , Surajo Salisu Musa Hassan. Ya ce Mustapha Salisu, Basiru Abubakar da Muhammad Rabiu ne suka ji rauni a harkokin ƴan bindigan.
Discussion about this post