Akalla mutum 7 ne ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Karfi dake karamar hukumar Takai a jihar Kano.
Mazauna kauyen sun ce maharan sun yi garkuwa da dagacen kauyen sannan wasu mutum uku sun ji rauni a dalilin harin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Kiyawa ya ce rundunar ta fara farautan waɗannan ƴan bindiga.
A ranar Laraba wani dan jarida a kauyen Sale Hussaini ya ce mahara dauke da muggan makamai sun afka kauyen da misalin karfe 11 daren Asabar inda suka zarce kai tsaye zuwa gidan dagace Abdul-Hayatu Ilu suka waske da shi.
Hussain ya ce daya daga cikin mutum bakwai din da maharan suka kashe makwabcin Abdul-Hayatu Ilu ne kuma maharan sun kashe shi ne saboda ihun rika yi a lokacin da aya gansu.
Ya ce maharan sun kashe mutum biyar a kauyen Tudun Makama.
Husaini ya ce mutane bakwai din da maharan suka kashe sun hada da Tasi’u Birniyo, Ali Yahaya,
Hashimu Amo, Sadiqu Hussaini, Ahmadu Danlanbu, Bala Audu da Shu’aibu Agwar-maji.
Mutanen da suka ji rauni na asibitin Birnin Kudu dake jihar Jigawa likitoci na duba su.
Jihar Kano na daya daga cikin jihohin Arewa da bata fama da hare-haren ‘yan bindiga a kasar nan.
Jihohi irin su Katsina, Zamfara, Kaduna ne ke yawan fama da hare-haren ƴan bindiga.