Hukumar Kula da Ayyukan Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta gayyaci Hukumar EFCC domin yin cikakken binciken bankaɗo zargin yin hajijiya da kuɗaɗen da maniyyata ke tarawa a ƙarƙashin Asusun Adashen Tara Kuɗaɗen Maniyyata (Hajj Savings Scheme).
A ranar Juma’a ce NAHCON ta bayyana cewa za ta rubuta wa EFCC wasiƙar gayyata domin jami’an ta su bankaɗo zargin yin hajijiya da kuɗaɗen da maniyyata ke tarawa a hankali kafin ranar tafiya aikin Hajji ta yi.
Maniyyata da ba su iya haɗawa ko biyan kuɗin aikin Hajji a lokaci ɗaya, sai NAHCON ta buɗe masu asusun adashen da za su riƙa saka kuɗi su na tarawa a hankali, a wani Asusun Ajiyar Jaiz Bank.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa NAHCON ta shiga tsomomuwa, bayan da wani rahoto da wata jarida ta buga, ya yi zargin cewa wasu jami’ai na dangwala hannaye cikin asusun su na dulmiyo kuɗaɗe, su na tsotse hannayen su.
Kuɗaɗen dai na karo-karo ne da masu fatan tafiya Hajji ke tarawa a hankali.
Majalisar Tarayya ce ta nemi a yi binciken, sannan kuma ta bayar da umarnin a dakatar da ajiye kuɗaɗen adashe a cikin asusun, domin a samu damar yin binciken ƙwaƙwaf a gano adadin da suka salwanta.
An ƙaddamar da Asusun Adashen Maniyyata cikin Oktoba, 2020, kuma NAHCON ɗin ce ta ƙirƙiro shi tare da haɗin guiwa da Bankin Jaiz. An yi haka ne domin sauƙaƙa wa masu ƙaramin ƙarfi samun damar tara kuɗaɗen zuwa aikin Hajji sannu a hankali a cikin shekara ɗaya.
Majalisar Tarayya ta ce shirin na Asusun Adashen Tara Kuɗin Hajji akwai nuƙu-nuƙu a cikin harkar.
“Idan dai ba a yi wa rufƙar hanci ba, to lamarin zai kai ga cin hanci da kuma take doka a ɓangaren masu kula da asusun.”
A ɓangaren ta, NAHCON ta ce ta na maraba da EFCC ta zo ta yi bincike, domin babu wata harƙalla ko nuƙu-nuƙu wajen tafiyar da kuɗaɗen.
Cikin wata sanarwa da Jam’iar Yaɗa Labarai ta NAHCON, Fatima Usara ta sa wa hannu a ranar Juma’a, ta ce “NAHCON na goyon bayan gayyato EFCC domin yin bincike”, kamar yadda Kwamitin Majalisar Tarayya mai kula da Harkokin Aikin Hajji ya umarci a yi.
Ta ƙara da cewa duk wani mai tara kuɗin sa a cikin Asusun Adashen Tara Kuɗaɗen Maniyyata ya na ganin saƙon ‘alert’ a wayoyin su, na adadin kuɗin da ya ke tarawa da kuma duk ribar da aka samu idan banki ya juya kuɗaɗen, kowa na ganin ‘alert’ na kason sa daga cikin ribar.” Inji Fatima Usara.
Usara ta ce haka nan kuma a kai a kai NAHCON ta bayar da bayanan halin da asusun adashen ke ciki ga Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jiha, a kowace jiha daga jihohin ƙasar nan baki ɗaya.
“Ko cikin watan Maris sai da NAHCON ta bayar da waɗannan bayanai, kuma ta sanar da ribar da aka samu, tare da raba wa kowane mai ajiya a asusun daidai gwargwadon haƙƙin ribar sa. Kuma sun ga ‘alert’ na abin da suka samu.”
Hajijiya Da Kuɗaɗen Adashen Maniyyata: An Ciri Kuɗaɗe, Amma A Cinye Ba -NAHCON:
Fatima Usara ta ce, zargin ana kwashe kuɗaɗen kuma ba gaskiya ba ne.
“Dukkan waɗannan kuɗaɗen da maniyyata ke tarawa su na can a Bankin Jaiz ajiye.
“Kai ko a tsawon shekaru biyu da ba a je aikin Hajji ba (saboda korona), kuɗaɗen Hajjin yawancin jihohi sun kasance ajiye a asusun Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, kuma sai da NAHCON ta nuna masu rashin dacewar hakan. Ta ce sun karya doka.
“Sai fa Jihar Adamawa da ta tara naira miliyan 500, Bauchi miliyan 327.5, Barno miliyan 100, Edo miliyan 124, Gombe miliyan 350, Kogi miliyan 26.6, Nasarawa miliyan 252, Neja miliyan 433, Osun miliyan 150, Oyo miliyan 200, Taraba miliyan 400, Yobe miliyan 400, sai Rundunar Sojojin Najeriya miliyan 320.
“Kuɗaɗen waɗannan jihohi su ka tara sun kai naira biliyan 3.58, kuma sun kasance ajiye a Babban Bankin Najeriya (CBN), sai fa cikin wannan shekarar ce aka maida wa kowace jiha kuɗaɗen.” Haka dai NAHCON ta bayyana.