Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya ce tunda dai Shugaba Muhammadu Buhari ya lale katin yi wa manyan ɓarayin gwamnati afuwa, to ya rushe hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, wato EFCC da ICPC.
Wike ya ce Buhari ya wulaƙanta hukumomin EFCC da ICPC, ya kunyata su, ya kwance masu zani a kasuwa, bayan ya yi wa manyan ɓarayin gwamnati biyu afuwa.
Kalaman Wike na cikin wawa sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran sa mai suna Kelvin Ebiri ya sa wa hannu a ranar Litinin.
Wike wanda shi ma ya fito neman a tsayar da shi ɗan takarar PDP a zaɓen shugaban ƙasa, ya ce afuwar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa tsoffin gwamnonin biyu ya kashe duk wata daraja da martabar shirin yaƙi da cin hanci da shawara, kuma ya ɓata lokaci da ƙoƙarin da ɓangaren Shari’a ya shafe shekara da shekaru ya na yi.
Wike ya ce Buhari ya saki ɗaurarru biyun ne don kawai idan sun fito su taimaka wa APC cin zaɓen 2023.
“Idan Shugaba Buhari ya san bai shirya yaƙi da cin hanci da rashawa ba, to kawai ya rushe EFCC da ICPC, saboda ya lalata duk wata ƙima da hukumomin b CGiyu ke da ita. Kuma ba wanda zai ƙara yi masu kallon arziki.”
PREMIUM TIMES Hausa ta buga rahoton yadda wasu jami’an EFCC da ICPC suka ce Buhari ya kashe masu jiki, sun zama abin dariya ana yi masu gwalo.
Wasu jami’an Hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC sun bayyana cewa yanzu sun zama abin dariya, ba za a sake kallon su da daraja ba, ballantana a ɗauki aikin su da muhimmanci, tunda Shugaba Muhammadu Buhari ya na yin afuwa ga gaggan ɓarayin da suka kamo, bayan an ɓata shekaru masu yawa a kotu har aka ɗaure su.
PREMIUM TIMES ta yi hira da wasu jami’an hukumomin na yaƙi da cin hanci biyu daban-daban, kuma duk su ka nemi a sakaya sunan su.
“A baya ɓangaren shari’a mu ke kallo ke kawo cikas wajen samun nasarar daƙile cin hanci da rashawa. Amma yanzu kuwa ta fito fili cewa Shugaba Buhari ne ba shi da kishin daƙile wannan babbar matsalar.”
Da yawan waɗanda aka yi hirar da su a ɓangaren EFCC da ICPC, sun ce, “Buhari ya kashe mana jiki. Ba mu da sauran dukan ƙirjin tabbacin samun nasara. Yanzu sai dai mu juri zuwa ofis aiki don karɓar albashi kawai, amma babu sauran shauƙin yaƙi da cin hanci da rashawa a zuciyar mu.”
Waɗannan kakkausan kalamai sun fito ne biyo bayan Shugaba Buhari ya yafe wa tsoffin gwamnoni biyu, Joshua Dariye na Filato da Jolly Nyame na Taraba.
Buhari ya yi masu afuwar ɗaurin da Kotun Ƙoli ta jaddada a kan su, bisa dalili na tsufa da kuma rashin lafiya.
Buhari wanda ya hau mulki albarkacin romon-kunnen da ya yi wa ‘yan Najeriya cewa zai yaƙi cin hanci da rashawa, ya janyo wa kan sa tsangwamar da an daɗe ba a yi masa irin ta ba, bayan ya yi afuwa ga manyan ɓarayin da suka sace kuɗaɗen talakawan su.
“Yanzu maimakon a riƙa jin tsoron mu saboda irin aikin da mu ke yi, za su koma ana yi mana dariya da gwalo, ana ganin ɓata lokacin mu kawai za mu riƙa yi, ko mun kamo mai laifi ma Buhari zai iya yi masa afuwa.
“Abin da ya fi ba mu takaici shi ne yadda mu ke yin baƙin jini a wurin manya. Sannan a zo a yanke wa mutum hukuncin ɗaurin shekaru, sannan a ce an yafe masa.
“Dubi dai yadda aka ɓata kusan shekaru 10 ana jeƙala-jeƙalar shari’a a kotu. An kashe kuɗaɗe, an ɓata lokaci. Kuma abin mamaki fa waɗanda aka kama da laifin satar ce suka riƙa ɗaukaka ƙara har zuwa Kotun Ƙoli, amma ba su yi nasara ba.”
Wani kuma jami’in da mamaki ya dame shi, cewa ya yi “Anya Buhari kuwa ya karanta illar wannan kasassaɓar da ya yi?”
“Mun sadaukar da rayukan mu, mun rasa abokan mu saboda yanayin aikin mu. Amma yanzu Buhari ya rushe mana gini.”
Yayin da ake ci gaba da yin Allah-wadai da afuwar, babban lauya kuma ɗan kishin haƙƙin jama’a, Mike Ozekhome ya ce, “abin da Buhari ya yi ya ƙara tabbatar da zargin da ‘yan Najeriya ke yi cewa yaƙi da cin hanci da rashawa da Buhari ke yi, sai wanda aka raina ko ba a tare da shi ne doka ke hawa kan sa.”
Tuni dai ƙungiyoyi irin su CISALC, TI, SERAP da wasu da dama ke ta kira ta jijijiga Buhari su na ƙoƙarin tayar da shi daga barci domin ya sake tunani, kuma ya soke wannan afuwa da ya yi wa manyan ɓarayin gwamnati.
PREMIUM BUHARI Hausa ta buga labarin cewa, bayan Buhari ya yafe wa Joshua Dariye tare da yi wa Jolly Nyame afuwa, ya kuma yi afuwa ga waɗanda su ka shirya juyin mulkin 1990, har suka yi yunƙurin raba Arewa daga Najeriya.
Haka kuma Buhari ya yi afuwa ga kwamandan soja laifin ɗauri saboda tserewa daga artabu da Boko Haram.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yafe wa tsohon Kwamandan Soja, Enitan Ransome-Kuti, Kwamandan Sojojin Haɗin-guiwar MJTF, wanda aka ɗaure saboda laifin dafe ƙeya ya tsere, ya kasa tunkarar Boko Haram.
An ɗaure shi cikin watan Janairu 2015, zamanin mulkin Goodluck Jonathan.
Enitan ɗa ne ga gogaggen ɗan taratsin nan marigayi Beko Ransome-Kuti, kuma ɗan’uwa ga Fela Ransome-Kuti.
An yafe masa shi da wasu mutum 162, ciki har da tsoffi gwamnoni biyu, Joshua Dariye na Filato da Jolly Nyame na Taraba, waɗanda aka ɗaure kotu ta kama su dumu-dumu da laifin satar biliyoyin kuɗaɗen da za a yi wa talakawan jihohin su ayyukan inganta rayuwa.
Kotun Musamman ta Sojoji ce ta kama Enitan da laifi kasa zuwa ya tunkari Boko Haram, a lokacin ya na Kwamandan MJTF a Baga, Jihar Barno.
A lokacin dai Enitan ya tsere, amma aka kamo shi, aka tsare, sannan aka yanke masa hukuncin ɗaurin wata shida kuma aka rage masa igiya daga Burgediya-Janar zuwa Kanar. Bayan nan kuma aka kore shi daga aikin soja.
PREMIUM TIMES ta gano cewa an janye hukuncin na sa ne bisa dalili na tausayi.
Fitaccen mai kare haƙƙin jama’a Femi Falana ne lauyan Enitan da wasu sojoji 60. Kuma shi ya rubuta wasiƙar neman a jingine hukuncin da aka yi masu.
Daga nan ne Majalisar Sojojin Najeriya ta soke ɗaurin watanni shida na Enitan Ransome-Kuti, sauran sauran sojoji 60 da aka yanke wa hukuncin kisa kuwa, aka rage zuwa ɗaurin shekaru 10, sanadiyyar wasiƙar da Femi Falana ya rubuta.
Daga nan kuma ya rubuta wasiƙa ga hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Kwamitin Shugaban Ƙasa, ya nemi ya ma yafe masu baki ɗaya.
Falana ya rubuta wasiƙar neman a soke hukuncin, kuma a yi masu afuwa, saboda su na da dalili ko hujjar guduwa daga yaƙi da Boko Haram.
Hujjar da Femi Falana ya kafa ita ce, sun gudu ne saboda an kasa samar masu da ingantattun makaman da za su iya tunkarar Boko Haram da su.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Buhari ya yafe wa Dariye, Nyame laifin satar kuɗin talakawa, ya yi wa wasu 157 afuwa.
Majalisar Ƙolin Najeriya ƙarƙashin ikon Shugaba Muhammadu Buhari ta yafe wa tsohon Gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye da tsohon Gwamnan Taraba, Jolly Nyame, waɗanda yanzu haka ke ɗaure a kurkuku, bayan yanke musu hukuncin satar maƙudan kuɗaɗen talakawan jihohin su.
Gwamnonin biyu a cikin mutum 159 da aka yafe wa laifukan da su ka aikata, a taron da Majalisar Ƙoli ta yi ranar Alhamis a Fadar Shugaban Ƙasa.
Daga cikin sauran waɗanda aka yafe wa ɗin, akwai tsohon janar kuma Minista a zamanin mulkin Abacha, Tajudeen Olariwaju, Kanar Akiyode, tsohon hadinin Mataimakin Abacha, watau Janar Oladipo diya da sauran dukkan jami’an sojojin da aka ɗaure waɗanda aka kama da laifin yunƙurin juyin mulkin Gideon Orkar, cikin 1990.
Majiya daga Fadar Shugaban Ƙasa ta ce an yafe wa Dariye da Nyame ne bisa dalillai na rashin lafiya da kuma tsufa.
Shekarun Nyame 66, ya yi Gwamnan Jihar Taraba daga 1999 zuwa 2007. An ɗaure shi shekaru 12 a kurkukun Kuje. A cikin 2020 ne Kotun Koli ta jaddada amincewa da ɗaure shi.
Shi kuma Dariye shekarun sa 64. Ya yi Gwamnan Filato daga 1999 zuwa 2007, ya na kurkuku ne saboda satar Naira biliyan 2. An ɗaure shi ya na sanata cikin 2018. Amma bai tafi kurkuku ba har sai da ya kammala wa’adin sa cikin 2019.
Da farko kotu ta ɗaure shi shekaru 14, amma Kotun Ƙoli ta maida hukuncin shekaru 10.
Taron Majalisar Ƙoli dai ya samu halartar dukkan tsoffin shugabannin Najeriya da ke raye, in bada Olusegun Obasanjo, wanda a yanzu haka ke Amurka ana duba lafiyar su.
Su Wane Mambobin Majalisar Ƙoli:
1. Shugaban Ƙasa (shugaban majalisa).
2. Mataimakin Shugaban Ƙasa (mataimakin shugaban majalisa).
3. Dukkan tsoffin shugabannin Najeriya na dimokraɗiyya da na soja.
4. Dukkan tsoffin Shugabannin Kotunan Najeriya.
5. Shugaban Majalisar Dattawa.
6. Kakakin Majalisar Tarayya.
7. Dukkan gwamnoni masu mulki a yanzu.
8. Antoni Janar na Tarayya, Ministan Shari’a na yanzu.