Wasu jami’an Hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC sun bayyana cewa yanzu sun zama abin dariya, ba za a sake kallon su da daraja ba, ballantana a ɗauki aikin su da muhimmanci, tunda Shugaba Muhammadu Buhari ya na yin afuwa ga gaggan ɓarayin da suka kamo, bayan an ɓata shekaru masu yawa a kotu har aka ɗaure su.
PREMIUM TIMES ta yi hira da wasu jami’an hukumomin na yaƙi da cin hanci biyu daban-daban, kuma duk su ka nemi a sakaya sunan su.
“A baya ɓangaren shari’a mu ke kallo ke kawo cikas wajen samun nasarar daƙile cin hanci da rashawa. Amma yanzu kuwa ta fito fili cewa Shugaba Buhari ne ba shi da kishin daƙile wannan babbar matsalar.”
Da yawan waɗanda aka yi hirar da su a ɓangaren EFCC da ICPC, sun ce, “Buhari ya kashe mana jiki. Ba mu da sauran dukan ƙirjin tabbacin samun nasara. Yanzu sai dai mu juri zuwa ofis aiki don karɓar albashi kawai, amma babu sauran shauƙin yaƙi da cin hanci da rashawa a zuciyar mu.”
Waɗannan kakkausan kalamai sun fito ne biyo bayan Shugaba Buhari ya yafe wa tsoffin gwamnoni biyu, Joshua Dariye na Filato da Jolly Nyame na Taraba.
Buhari ya yi masu afuwar ɗaurin da Kotun Ƙoli ta jaddada a kan su, bisa dalili na tsufa da kuma rashin lafiya.
Buhari wanda ya hau mulki albarkacin romon-kunnen da ya yi wa ‘yan Najeriya cewa zai yaƙi cin hanci da rashawa, ya janyo wa kan sa tsangwamar da an daɗe ba a yi masa irin ta ba, bayan ya yi afuwa ga manyan ɓarayin da suka sace kuɗaɗen talakawan su.
“Yanzu maimakon a riƙa jin tsoron mu saboda irin aikin da mu ke yi, za su koma ana yi mana dariya da gwalo, ana ganin ɓata lokacin mu kawai za mu riƙa yi, ko mun kamo mai laifi ma Buhari zai iya yi masa afuwa.
“Abin da ya fi ba mu takaici shi ne yadda mu ke yin baƙin jini a wurin manya. Sannan a zo a yanke wa mutum hukuncin ɗaurin shekaru, sannan a ce an yafe masa.
“Dubi dai yadda aka ɓata kusan shekaru 10 ana jeƙala-jeƙalar shari’a a kotu. An kashe kuɗaɗe, an ɓata lokaci. Kuma abin mamaki fa waɗanda aka kama da laifin satar ce suka riƙa ɗaukaka ƙara har zuwa Kotun Ƙoli, amma ba su yi nasara ba.”
Wani kuma jami’in da mamaki ya dame shi, cewa ya yi “Anya Buhari kuwa ya karanta illar wannan kasassaɓar da ya yi?”
“Mun sadaukar da rayukan mu, mun rasa abokan mu saboda yanayin aikin mu. Amma yanzu Buhari ya rushe mana gini.”
Yayin da ake ci gaba da yin Allah-wadai da afuwar, babban lauya kuma ɗan kishin haƙƙin jama’a, Mike Ozekhome ya ce, “abin da Buhari ya yi ya ƙara tabbatar da zargin da ‘yan Najeriya ke yi cewa yaƙi da cin hanci da rashawa da Buhari ke yi, sai wanda aka raina ko ba a tare da shi ne doka ke hawa kan sa.”
Tuni dai ƙungiyoyi irin su CISALC, TI, SERAP da wasu da dama ke ta kira ta jijijiga Buhari su na ƙoƙarin tayar da shi daga barci domin ya sake tunani, kuma ya soke wannan afuwa da ya yi wa manyan ɓarayin gwamnati.