Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta fatattaki daruruwan masu tsintar bola dake gararamba a Abuja.
Rundunar ta gabatar da matasan ne wadanda ta kama a kusurwa daban da ban a babban birnin tarayya, Abuja.
Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan Abuja Ben Igwe ya ce rundunar ta yi haka ne saboda jitajitar darkakowar bakin matasa zuwa cikin garin Abujan wanda ba a san sana’ar su ba kuma su saje da ‘yan bolan suna tafka ta’adi a garin.
Ya ce rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wadanda ta samu da laifi.
“Abuja ba garin kowani irin mutum bane. Ba garin ‘yan bola bane saboda haka ba za a zuba musu ido ba su shigo suna amfani da sana’ar tsintar bola suna aikata munanan ayyuka.
Igwe ya ce an kama masu tsintar bola a Abuja da wasu kayayyakin da ba a bola suka tsince su ba, kayan sata ne.
“Mun umarci masu tsintar bola su koma inda suka fito, Abuja ba garin su bane. Mun umarci mutane su sanar da ‘yan sanda idan suka ga wani na yawon roron bola a Abuja daga yanzu.
Abin da doka ta ce
Wani lauya a Abuja Abduljalil Musa ya ce koran ‘yan roran bola da rundunar ‘yan sandan Abuja ke shirin yi ya saba wa tsarin dokar Najeriya ta shekarar 1999.
Musa ya ce bisa ga tsarin doka kowani dan Najeriya na da ‘yancin zama a duk inda yake so ba tare da fargaban komai ba.
Ya ce koran su daga garin Abuja da ‘yan sanda ke kokarin yi tauye musu hakki ne.