‘Yan bindiga sun kashe mutum uku sannan suka yi garkuwa da mutane da dama a kauyen Baba Juli dake karamar hukumar Bali a jihar Taraba.
Maharan sun afka kauyen yayin da mutane ke yin bude bakin azumin wannan rana.
Idan ba a manta ba a watan da ya gabata ‘yan bindiga sun kai hari kauyen amma ‘yan kungiyar sakai suka fatattake su.
Wani mazaunin kauyen da da baya so a fadi sunan sa ya ce ‘yan bindigan sun kawo musu harin bazata ba domin sun afka kauyen yayin da mutane ke bude baki.
“A lokacin da ‘yan bindigan suka shigo babu abinda muka iya yi domin sun kawo mana harin ban zata ne.
“Maharan sun kashe mutane uku sannan sun yi garkuwa da mutane da dama.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Usman Abdullahi ya tabbatar da hari.
Discussion about this post