‘Yan bindiga sun kashe mutane da dama sannan sun cinna wa gidaje wuta a kauyuka hudu dake karamar hukumar Kanam a jihar Filato.
Wannan abin ban tsoron ya auku ne a ranar Lahadi.
Wani mazaunin karamar hukumar Dankadi Dukup ya ce mutane da dama sun rasa rayukan su sannan wasu da dama sun ji rauni a jikin su a dalilin harin.
Dukup ya ce zuwa yanzu mutane da dama sun gudu sun bar gidajen su.
Bayan haka jami’in yada labarai na rundunar Operation safe Haven OPSH Ishaku Takwa shima ya tabbatar da harin wa manema labarai a ranar Lahadi a garin Jos.
Sai dai a bayanin da ya yi Takwa bai fadi adadin yawan mutanen da suka mutu ko suka ji rauni a dalilin wannan hari ba.
Takwa ya ce zaman lafiya ya soma dawowa kayukan saboda gwamnati ta aika da jami’an tsaro.
Wannan hari ya faru bayan awowi 24 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ‘ya da uwar gidan kwamishinan muhalli na jihar.
Idan ba a manta ba a makon da ya jiya ‘yan bindiga sun kashe mutum 10 wasu mutum 19 sun ji rauni a wajen wani taron buki da aka yi a masarautar Irigwe dake garin Chando Zerreci, karamar hukumar Bassa.
Maharan sun kawo farmaki wannan kauye ne a lokacin da mutanen kabilar iregwe ke taron bikin ‘Zerreci’, wato taron shiga lokacin damina.
Wadanda suka ji rauni na a asibitin Enos dake Miango.
Jami’in yada labarai na kungiyar matasan Irigwe Lawrence Zango ya yi kira ga dukan sassan gwamnati da su taimaka wajen samar wa kauyen Irigwe tsaro.