Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa a shekarar 2021 mutum 111,062 ne suka kamu mutum 3,604 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar amai da gudawa a Najeriya.
Kungiyar ta ce hakan ya nuna cewa Najeriya ta samu karuwa a yaduwar cutar fiye da yadda aka samu a shekarar 2020 da shekarun da suka gabata.
Wakilin WHO a Najeriya Walter Mulombo ya sanar da haka a taron inganta yin allurar rigakafin cutar da aka yi da hukumar GTFCC a Abuja ranar Litini.
Hukumar GTFCC hukuma ce dake karkashin inuwar WHO dake taimakawa wajen yaki da cutar musamman a kasashen da ya fi barkewa.
Mulombo ya yaba wa namijin kokarin da GTFCC ke yi wajen yaki da cutar a Najeriya musamman ta hanyar wayar da kan mutane mahimmancin tsaftace muhalli da ruwan da suke amfani da shi domin samun kariya daga kamuwa da cutar.
“ Hukumar ta taimaka wajen yi wa mutum miliyan 1.7 allurar rigakafin cutar a jihohin Bauchi-, Zamfara , Jigawa da Yobe.
Abubuwa 10 dake haddasa barkewar cutar a kasar nan
1. Rashin tsafta da barin ƙazanta a gida, musamman abinci da kayan abinci ko kwanukan cin abinci.
2. Zubar da tulin shara da bola aikin unguwanni, wadda ruwan sama ke maida ƙazantar ta s cikin jama’a.
3. Zubar da shara ko bola ko bayan gida a cikin ƙaramu da magudanan ruwa..
4. Yin bayan gida a fili ko a kan bola.
5. Rashin ruwa mai tsafta a cikin al’umma.
6. Ƙarancin asibitocin kula da marasa lafiya a cikin jama’a marasa galihu.
7. Ƙaranci ko rashin magungunan da za a bai wa mai cutar kwalara cikin gaggawa.
8. Matsalar ƙarancin jami’an kiwon lafiya a cikin jama’a..
9. Rashin hanyoyi masu kyau da za a garzaya asibiti da mai cutar amai da gudawa cikin gaggawa.
10. Shan ruwan ƙarama ko kogi, wanda ake zubar da shara, kashin dabbobi da kuma bayan gida.
Discussion about this post