‘Yan bindiga sun kai hari wasu kauyukan dake kananan hukumomin Gassol da Karim Lamido a jihar Taraba.
Kamar yadda gidan jaridar ‘Daily Trust’ ya buga ‘yan bindigan sun kai hari ofishin ‘yan sanda dake kauyukan inda suka fatattaki ‘yan sanda dake ofishin.
Jaridar ta rawaito cewa ‘yan bindigan na yi wa mata da ‘yan mata fyade tare da yin garkuwa da mutane da dama daga kauyukan.
A dalilin wannan hari mazauna kauyukan Gwammo, Wurno, Tungan Kaya, Gidan Kawoyel da Ali Kwala duk sun gudu sun bar gidajen su.
Sannan mazaunan dake kauyukan WuroJam, Karar, Shika, Amar, Zip, WuruJam, Illela da Maigemu na fargaban cewa maharan za su kawo musu hari nan ba da dadewa ba.
Wani mazaunin garin Kambari da baya so a fadi sunan sa ya bayyana wa gidan jaridar cewa mazauna garin na samun mafaka a Mutum biyu da sauran wurare saboda hare-haren ‘yan bindiga.
Mutumin ya ce zuwa yanzu babu jami’an tsaro a garin sannan ‘yan bindigan da ake zaton daga jihohin Zamfara da Katsina suke na yawo da makaman su a fili ba tare da fargaba ba ko za su iya cin karo da jami’an tsaro ba.
Yadda sojoji suka fatattaki ‘yan bindiga
Sojoji sun yi bata kashi da ‘yan bindigan inda suka kashe da dama a karamar hukumar Gassol.
Wani mazaunin garin Rabiu Saidu ya ce fatattakar ‘yan bindigan da sojojin suka yi ya kwantar wa mutane da hankalinsu a garin.
Saidu ya yi kira ga gwamnati da ta aika da jami’an tsaro zuwa garin Kambari da kauyukan dake tsallaken Rafin Benue domin gamawa da ‘yan bindigan da suka addabi mutanen yankin.