‘Yan bindiga sun kashe mutum 10 wasu mutum 19 sun ji rauni a wajen wani taron buki da aka yi a masarautar Irigwe dake garin Chando Zerreci, karamar hukumar Bassa.
Jami’in yada labarai na kungiyar matasan Irigwe Lawrence Zango ya sanar da haka a garin Jos ranar Lahadi.
Zango ya ce maharan sun kawo farmaki wannan kauye ne a lokacin da mutanen kabilar iregwe ke taron bikin ‘Zerreci’, wato taron shiga lokacin damina.
Ya ce zuwa yanzu wadanda suka ji rauni na a asibitin Enos dake Miango.
Ya yi kira ga dukan sassan gwamnati da su taimaka wajen samar wa kauyen Irigwe tsaro.
” Muna kira ga gwamnati da ta gudanar da bincike kan yawan hare-haren da ake kawo wa kauyen domin ganin ta hukunta duk wadanda ke da hannu a tada rikicin sannan da biyan diyya ga duk wadanda rikicin ya shafa.
“Ya zama dole gwamnati ta dauki tsauraran matakai domin kare rayuka da dukiyoyin mutanen Irigwe.
Zango ya yi kira ga masu fada a ji na kasashen waje da su taimaka wajen kawo karshen kisan rayukan da ake yi a jihar Filato.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ubah Ogaba ya tabbatar da wannan hari sannan ya ce rundunar ta aika da ma’aikata masarautar Irigwe domin samar da tsaro.
Ogaba ya kuma yi kira ga mutanen masarautar da su ci gaba da kiyaye dokoki cewa rundunar za ta ci gaba da aiki tukuru domin ganin ba a sake fadawa cikin irin wannan hali ba.
Discussion about this post