Babban bankin Najeriya CBN ya kirkiro da tsarin POS a shekarar 2013 domin saukake cinkoson banki sannan da baiwa mutane musamman talakawan mazauna karkara damar damawa da su a harkar kasuwancin kudi cikin sauki.
CBN na da burin saka akalla kashi 80% na mutane musamman matasa cikin harkan kasuwancin da hada-hadar kudi domin ganin tattalin arziki kasa ya bunkasa.
Sai dai kuma wannan burin na CBN na neman ya durkushe saboda hare-haren ‘yan bindiga a yankin Arewa musamman a jihar Sokoto.
A karamar hukumar Goronyo dake jihar Sokoto Wani Abbas Muhammed dake sana’ar kasuwancin kudi na POS ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka karya shi.
Karamar hukumar Goronyo na daga cikin kananan hukumomin da suka yi kaurin suna wajen fama da hare-haren ‘yan bindiga a jihar Sokoto.
Muhammed ya ce ya fara sana’ar POS bayan da aka kore shi daga aikin koyarwa da ake yi a karamar hukumar.
Ya ce ya ranci kudi daga wasu abokan sa da ‘yan uwa sai ya bude sana’ar PoS amma a cikin dare daya ‘yan bindiga suka kawo hari gidan sa suka tafi da naira miliyan 3.5, matarsa Zarau da yayansa Annas.
“Maharan sun bukaci naira miliyan biyar kudin fansa amma da suka ga bani da halin biya sai suka karbi Naira 300,000.
Muhammed ya ce tun da matarsa da yayansa suka dawo gida ya bar gidan da yake zama sannan ya dawo da shagon POS din sa kusa da gidan sa.
Shima Suleiman Adamu ya ce a dalilin hare-haren ‘yan bindiga yasa ya daina sana’ar POS ya koma cikin garin Sokoto yana zama tare da iyalinsa.
Adamu ya ce kafin ‘yan bindiga su kawo masa hari yana da shago a cikin kasuwan dake ci mako-mako sannan Yana taimakawa ‘yan kasuwa wajen saka kudaden su a cikin asusunsu, ciro kudi a asusu sannan da aika wa ‘yan uwansu kudi.
“Tun da ‘yan bindiga suka kawo min hari na ga cewa raina ya fi kowace dukiya a duniya. A dalilin haka na bar sana’ar.
Wani Suraju Umar wanda hare-haren ‘yan bindiga ya illata masa sanar sa na POS ya ce yanzu mutane basu zuwa karamar hukumar Goronyo saboda ‘yan bindiga.
Yadda hareharen ‘yan bindiga ya tarwatsa harkokin mazaunan karamar hukumar Goronyo
Wata mai siyar da kaya a kasuwa Zainab Aliyu ta bayyana cewa a da suna amfani da POS wajen ciro, ajiya, aikawa da kudi da biyan wasu bukatunsu, amma hare-haren ‘yan bindiga ya hana su yanzu.
Wani dan sanda dake a karamar hukumar Ismail Muhammed ya ce hare-haren ‘yan bindiga ya hana mutane da dama shiga cikin harkan kasuwancin kudi domin a yanzu haka babu banki dake aiki sannan masu sana’ar POS na rufe shagunan su.
“Akwai lokacin da mutane a garin nan ke aika na cikin garin Sokoto domin na aika wa ‘ya’yan su dake makaranta kudi
Muhammed ya ce harkan kasuwancin kudi ya gurgunta a wannan bangare na jihar Sokoto.
Kwararriya a harkokin kasuwancin kudi Ayodeji Ajao ta bayyana cewa rashin tsaro na gurgunta tattalin arziki kasar nan wanda idan ba an yi gaggawar gamawa da ‘yan bindiga bane za a cigaba da samunkoma baya bunkasar tattalin arzikin kasa.
Discussion about this post