A ranar Alhamis ne wata yarinya mai shekara 20 ta bayyana a kotun dake jihar Legas cewa mahaifinta Akin Isacc ya rika yin lalata da ita har sai da ya dirka mata ciki.
Yarinyar ta bayyana cewa a baya da kakanta mace take zama kafin daga baya ta zo ta fara zama da mahaifinta.
Ta ce ta dawo da zama da mahaifinta a shekarar 2019 domin ya ce idan ta dawo tana zama da shi za ta rika zuwa makaranta da kuma samun kula.
Yarinyar ta ce Isacc ya fara lalata da ita tana da shekara 17 a lokacin gwamnati ta saka dokar zaman gida dole saboda barkewar annobar korona a shekaran 2020.
Ta ce Isacc wanda ke da mata biyu ya rika danne ta a gidan su dake Alapere.
“Idan har ban bada haɗin kai ba Isacc kan lakada min duka da wata dorina da ya siyo saboda ni sannan ya danne ni.
“Isacc ya zo ya hana ni zuwa cocin da na saba zuwa wato C&S ya tilasta ni wai sai cocin Redeemed ne zan rika zuwa.
“A watan Yuli na gano cewa Ina da ciki inda Isacc ya rika bani wasu kwayoyin magunguna tare da yi mun allura har guda 15 domin cikin ya zube amma bai yiwu ba.
“Daga nan sai Isacc ya kai ni wani waje da babu fitilla inda a nan ne aka cire mun ciki.
Yarinyar ta ce tun bayan da Isacc ya tabbatar an cire cikin ya rika hana ta fita, ya hana ta amfani da wayan salulan ta sannan ya hana ta ganin wanta da suka hada uwa daya.
“Isacc ya yi kokarin ya ci gaba da lalata da ni amma kulun ya zo sai na ki bashi hadin kai a dalilin haka ya sa kulun yake lakada mun duka.
“Da dukan ya yi yawa sai wasu makwabtan mu suka ce na zo na rika zama tare da su amma ko na zo sai na koma gida da zaran mahaifina ya dawo saboda suna taron shi saboda shi dan OPC ne.
A karshe dai hukuma ta tsare mahaifin sai an gama bincike akai