Duk da Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya sha sukar sarakunan gargajiya na jihar da laifin haɗin baki da ‘yan bindiga, hakan bai hana shi shirya ƙasaitaccen bikin yi masu watandar motocin alfarma ba, har guda 260.
An yi bikin rabon motocin samfurin Cadillac 2019 a Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara, bikin da aka gayyaci Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III a matsayin babban baƙo.
An yi bikin ranar Laraba, kwana biyu bayan ‘yan bindiga sun afka cikin garin Tsafe sun kashe mutane lokacin Sallar Tarawih a jihar. Cikin waɗanda aka kashe, har da ɗan Kwamishinan Harkokin Tsaro na Jihar Zamfara, Mamman Tsafe.
Shi da kan sa Matawalle ya sha zargin sarakunan gargajiya da ɓoye ‘yan bindiga ko goyon bayan su a asirce.
Cikin watan Oktoba, 2019 Matawalle ya kafa kwamiti a ƙarƙashin shugabancin tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Abubakar, wanda a cikin rahoton kwamitin kan matsalar tsaro, ya bada shawarar korar wasu sarakunan gargajiya da ya ce su na da haɗin baki da ‘yan bindiga.
Haka kuma kwamitin ya rattaba cewa aƙalla ‘yan bindiga sun karɓi naira biliyan uku matsayin kuɗaɗen fansar ɗimbin mutanen da su ke garkuwa da su.
A wurin bikin watandar motocin samfurin Cadillac 2019, an raba motocin na alfarma ga manyan sarakuna 17, manyan hakimai 13 da kuma hakimai 230.
Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamnan Zamfara, Zailani Bappa, ya ce Ma’aikatar Kula da Masarautu ce ta raba motocin, domin sarakuna su samu damar gudanar da ayyukan taimakawa wajen samar da tsaro a jihar.
Ya ce Gwamantin Zamfara ta kuma raba motoci 200 samfurin Totota Hilux ga jami’an tsaro, domin ƙara masu ƙwarin guiwa.
A wurin bikin raba motocin, Gwamna Matawalle ya jinjina wa sarakunan gargajiya wajen bayar da gudunmawar ƙoƙarin kawo ƙarshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Ya ce sarakuna ba ƙashin yadawa ba ne, su na da gagarimar rawar da su ke takawa a cikin al’umma.
Discussion about this post