‘Yan Najeriya sun cika da mamaki ganin yadda jam’iyya mai mulki APC, ta yanka farashin fam ɗin takarar shugabancin ƙasa kan naira miliyan 100.
Hakan ya sa PREMIUM TIMES ta yi ƙididdigar da ta nuna cewa kuɗin fam ɗin na takarar shugaban ƙasa sun zarce yawan albashin Shugaban Ƙasa kan sa na tsaron mulkin sa na shekaru bakwai.
Hakan ya sa jama’a na cike ta tambayar APC cewa ta yaya za ta bai wa mutum aiki amma kuma fam ɗin neman aikin ya fi tsadar albashin sa na shekara bakwai, ba ma na wata ɗaya ba?
Albashin Shugaban Ƙasa a Najeriya dai Naira miliyan 1.17 duk wata, ciki kuwa har da alawus-alawus ɗin sa. Amma tantagarya kuma gundarin albashin naira 292,892 ne. Sauran kuma duk alawus-alawus ne na haƙƙin aiki.
Haka albashin ya ke a Hukumar Raba Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa (RMAFC).
Ƙididdigar game-gari ta nuna albashin shugaban ƙasa a Najeriya Naira miliyan 14.05 a kowace shekara.
A cikin shekaru bakwai, Shugaban Ƙasa zai karɓi albashin naira miliyan 98.5.
A cikin shekaru huɗu, zai karɓi naira miliyan 56.2, kusan rabin kuɗin fam ɗin da ya saya na Naira miliyan 100 kenan.
Wato za ka sayi fam na Naira miliyan 100. Idan ka ci zaɓe, za a ba ka albashin shekaru huɗu na zangon shugaban ƙasa na farko.
Mutane da yawa fassara farashin fam ɗin da cewa wani salo ne na ɗaure wa satar kuɗin gwamnati gindi kawai.
Wasu kuma ganin cewa wani salo ne na hana wanda ba shi da ƙarfi fitowa ya nuna sha’awar tsayawa takarar shugabancin Najeriya.
Ga mai son tsayawa takara, banda kuɗin fam naira miliyan 100, akwai kuma gaganiyar kashe biliyoyin kuɗaɗe wajen kamfen yayin rangadin sassa, jihohi da yankunan karkara da sauran garuruwa.
Su na ɗaukar haya da shatar jiragen sama, ga kuɗaɗen kama otal-otal, ɗaukar ma’aikata, tallace-tallace, biyan mawaƙa, kama hayar gine-ginen ofisoshin ɗan takara a faɗin jihohin Najeriya da Abuja.
Sannan kuma akwai maƙudan kuɗaɗen da ake kashe wa wakilan jam’iyyar da za su yi zaɓe, wato ‘delegates’.
Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi alƙawarin daƙile cin hanci da rashawa tun kafin 2015, har yanzu bai ce komai ba, dangane da tsadar fam ɗin.
Hasali ma ya na zaune a Dakin Taro a otel ɗin Transcorp Hilton Hotel Abuja, Majalisar Zartaswa ta APC ta bayyana farashin fam ɗin naira miliyan 100.
A 2014, Buhari ya yi ƙorafi ganin cewa APC ta sayar da fam na takarar shugaban ƙasa, a kan naira miliyan 27.5. Buhari a lokacin ya ce fam ɗin ya yi matuƙar tsada. Har ya ce bashin banki ya ci sannan ya samu kuɗin sayen fam ɗin.
Hakan ya nuna farashin shiga takarar Shugaban Ƙasa a 2023, ya nunƙa na shekarar 2015 kusan da kashi 300%.
Har yanzu dai ɓangaren masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasa daga ɓangaren APC babu wanda ya yi ƙorafin cewa fam ɗin ya yi tsada.
Cikin makon jiya ne jam’iyyar PDP ta roƙi EFCC da ICPC su binciki duk ɗan APCin da ya lale naira miliyan 100 ya sayi fam na takarar shugaban ƙasa
Jam’iyyar PDP mai adawa da APC ta yi kira ga hukumomin yaƙi da rashawa, wato EFCC da ICPC su binciki duk wani ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC wanda ya tsige naira miliyan 100 ya sayi fam ɗin takara.
PDP har yau ta ce abinci duk wanda ya fitar da naira miliyan 50 daga APC ya sayi fam, domin a tantance yadda aka yi suka samu kuɗaɗen.
Haka nan kuma ta ce ya dace idan dai har yaƙi da cin hanci da rashawa su gurfanar da duk wanda ya sayi fam ɗin a kotu, su caje shi da laifin damfara.
“Rashin hankali ne tantagaryar a ce za a sayar da fam ɗin takara naira miliyan 100 da kuma naira miliyan 50. Duk wanda ya tsige kuɗi ya saya, to ɗan damfara ne, a maka shi kotu kawai.” Inji PDP.
Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayi ne ya yi wannan kiran da kan sa, cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran sa Simon Imobo-Tswam ya sa wa hannu, kuma ya fitar a ranar Alhamis.
Kalaman na Ayu sun fito ne bayan da APC ta bayyana Naira miliyan 100 ce kuɗin fam na takarar shugaban ƙasa.
APC ta raba kuɗin gida biyu. Naira miliyan 30 kuɗin na-gani-ina-so, naira miliyan 70 kuma kuɗin fam. Kuɗi sun kama naira miliyan 100 kenan.
Shi kuma duk mai don fitowa takarar gwamna a zaɓen-fidda-gwani, zai biya Naira miliyan 50. Yayin da sanata zai biya Naira miliyan 20, ɗan takarar Majalisar Tarayya kuma zai biya Naira miliyan 10.
Yayin da masu takarar Majalisar Dokokin Jihohi za su biya naira miliyan 2 kowanen su.
Sai dai kuma APC ta amince ta yi wa kowane ɗan takarar da bai kai shekaru 40 ba, an yi masa ragin kashi 50 bisa 100 na kuɗin.
Baragurbin Munafukai’:
PDP ta ce makudan kuɗaɗen da APC ta yanka a biya na sayen fam ɗin takara ya fassara APC da cewa baragurbi ce, kuma munafika.
“Yanzu ‘yan Najeriya za su iya gani ƙuru-ƙuru cewa APC ba wata tsiya ba ce, sai gungun wasu ‘yan ta-kifen da su ka haɗa kai don kawai su karɓe mulki, su ƙaƙaba wa jama’a ƙuncin rayuwar babu gaira babu dalili. Ba su damu ba har ‘yan jam’iyyar su ma ƙaƙaba masu masifar tsadar rayuwa suke yi.”