A daren Lahadin da ya gabata ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 22 a garin Jere dake kan titin Kaduna-Abuja, Jihar Kaduna.
Kakakin rundunar’yan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige bai amsa kira da sakonnin tes game da harin sai dai kuma tsohon sanata dake wakiltar Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani ya bayyana harin a shafinsa na Tiwita.
Sani ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da Alhaji Yusuf da iyalen sa, Alhaji Kasuwa da iyalen sa, Dantala Direba da iyalen sa, Sule Maishago da iyalen da wasu yara Almajirai.
Wani mazaunin garin Shehu Bala ya ce ‘yan bindigan sun shiga garin ne da misalin karfe 11 na dare inda suka dauki tsawo lokaci suna kwashe mutane daga gidajen su.
Bala ya ce mutum daya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su ya tsere.