Jami’in Kwastam Mu’awiya Gambo da faston darikan cocin katolika Felix Zakari na cikin mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a rukunin gidaje masu ƙananan kudi Low Cost dake Kofan Gayan da Gwangwaje dake Zariya jihar Kaduna.
Majiya da dama sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigan akan baburan sun dira unguwan Low-Cost da misalin karfe 9 na dare.
Wani mazaunin Zariya Aminu Dogo ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun tafi da dan jami’in Kwastam din mai suna Khalifa.
Dogo ya ce a shekarar 2021 ‘yan bindigan sun skawo farmaki unguwan Low-cost sun ji wa mata da yara kanana rauni da yawa.
Wani mazaunin Zariya Musa Abdulmalik ya ce ‘yan bindigan sun dade suna fakon Gambo su yi garkuwa da shi amma basu sami sa’an sa ba sai yanzu.
“Shi ya sa nake fada muku cewa akwai mutane da suke hada baki da ‘yan bindiga da suke tare da mu domin ba zan iya cewa sa’a ne suka samu ba ko sun yi shiri na musamman ne ba suka yi garkuwa da Ganbo.
Ma’aikacin gidan radiyon Queen FM dake Zariya Saifullahi Lawal ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da wata mata mai suna Jamila Abbas.
“Da jami’an tsaro suka zo sai ‘yan bindiga suka koma Gwargwaje suka ci gaba da kai wa mutane hari.
Lawal ya ce ‘yan bindigan sun yi awon gaba da mutane da dama a Gwargwaje.