Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe sojoji 11 da ‘yan kungiyar sa kai da gwamnati ta amince da su guda uku a karamar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna.
Rundunar ta sanar da haka ne a wani takarda da ta fitar wanda Sahara Reporters ta buga a shafinta.
Bisa ga takardar rundunar ta ce maharan sun far wa sansanin sojojin dake garin Polewire wanda ke hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna ranar Lahadi da misalin karfe 4:45 na yamma.
‘Yan bindigan sun yi amfani da manyan bindigogi masu cilla bama-bamai wajen kai wa sojojin hari.
Maharan sun bar sansanin sojojin da karfe 8 na dare tun da karfe 4:45 da suka fara barin wuta har sai da suka ci karfin sojojin dake barikin a wannan lokaci suka kashe su.
Zuwa karfe 9:15 na dare an aiko da wasu sojojin daga sansanin dake Gwaska domin kawo wa wadannan sojoji dauki sai dai basu iske su.
A dalilin wannan hari sojoji 19 da ‘yan kungiyar sa kai biyu sun ji rauni.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin yankin Arewa maso Yammacin Najeriya dake fama da hare-haren ‘yan bindiga da suka buwayi mazauna da matafiya a waɗannan jihohi
Discussion about this post