Kwamishinan Ƙananan Hukumomin Jihar Kano ya sauka daga muƙamin sa, zai nemi tsayawa takarar gwamnan Kano.
Garo, wanda ya yi ƙaurin-suna lokacin zaɓen gwamna a Kano, inda kama shi ya kekketa takardun ƙuri’un zaɓe, an zarge shi da laifin hargitsa ƙuri’un Mazaɓar Gama da ke cikin Ƙaramar Hukumar Nasarawa, lamarin da ta kai INEC ta ce zaɓen bai kammalu ba, ta kira shi ‘inconclusive’.
Kafin a soke zaɓen dai PDP ce kan gaba da ratar sama da ƙuri’u 20,000. Amma da aka sake na Gama da wasu mazaɓu, aka sanar APC ce ta lashe zaɓen.
A faɗin ƙasar nan dai an yi ta ƙorafin cewa fashi aka yi wa ɗan takarar PDP, Abba Kabiru-Yusuf.
Sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Ganduje ya fitar, ya ce Garo ya ajiye aikin sa domin ya nemi tsayawa takarar gwamnan Kano a zaɓen 2023.
Dokar Zaɓe Sashe na 84(12) ta 2022, ta ce tilas duk wani ma’aikatacin gwamnati ko mai riƙe da muƙamin siyasa, sai ya sauka daga muƙamin sa sannan zai tsaya takarar zaɓen fidda gwani.
Jam’iyyar APC dai ta sanar da INEC cewa za ta yi zaɓen fidda gwani tsakanin 30 da 31 ga Mayu.
Lokacin rikicin kekketa ƙuri’u a Mazaɓar Gama, an kama Garo tare da Mataimakin Gwamna Nasir Gawuna. Sai dai kuma an yi mamakin da ba a gurfanar da su kotu ba. A ƙarshe kuma kekketa ƙuri’u da su ka yi ce ta kai su ga nasarar lashe zaɓen.
Akwai aiki a gaban Garo, domin cikin waɗanda zai kara da su a zaɓen fidda-gwani, har da Sanata Barau Jibrin, wanda shi ma a ƙarshen makon jiya ne ya ƙaddamar da takarar sa a Kano.
Shi ma Kwamishina Nura Dankadai ya ajiye aiki domin fitowa takarar ɗan majalisar tarayya na Mazaɓar Ƙananan Hukumomin Doguwar da Tudun Wada.
Kwamishinan Raya Karkara Musa Iliyasu-Kwankwaso shi ma ya ajiye aiki domin fitowa takarar majalisar tarayya na Mazaɓar Ƙananan Hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam.
Aƙalla dai ana ganin sama da mutum 23 ke neman kujerar gwamnan Kano afujajan, daga jam’iyyu daban-daban.
Discussion about this post