Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Tarayya wasiƙar neman amincewa ya ƙara malejin kuɗaɗen tallafin fetur na shekarar 2022 zuwa naira tiriliyan 4.
A cikin wasiƙar wadda Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya karanta a zauren majalisa a ranar Alhamis, Buhari ya nemi a ƙara dala 11 a kan gejin kirdadon farashin litar ɗanyen mai a malejin kasafin kuɗin 2022, ta yadda za a shigar da kuɗaɗen tallafin mai da sauran buƙatun kashe kuɗaɗe a ciki.
Shugaba Buhari ya ce an ware naira biliyan 442.72 domin biyan kuɗaɗen tallafin mai a tsakanin Janairu zuwa Yuni, 2022. Amma kuma saboda tashin farashin ɗanyen man fetur a kasuwannin duniya, hakan ya sa Najeriya ta na biyan ƙarin kuɗaɗen tallafin fetur masu tarin yawa.
A kan haka ne wasiƙar Buhari ke ƙunshe da buƙatar neman ƙarin naira tiriliyan 3.557, ta yadda adadin kuɗaɗen tallafin mai na 2022 za su kai naira tiriliyan 4 cif-cif.
A yanzu dai Najeriya ta yi kasafin 2022 a kan kowace gangar ɗanyen man fetur a naira 62. Idan Majalisar Tarayya ta amince da roƙon da Buhari ya yi mata, to za a maida kasafin 2022 zuwa kowace gangar ɗanyen mai dala 73 kenan.
Sai dai kuma gwamnati na ta ƙoƙarin rage yawan ɗanyen mai da ta ke haƙowa a kullum. Za a rage haƙo lita 283,000 a kullum daga yawan ɗanyen mai da ake haƙowa, saboda matsalar masu fasa bututu su na satar mai.
Hakan ya na nufin za a riƙa haƙo ganga miliyan 1.6 a kullum, maimakon ganga miliyan 1.83 kenan.
Buhari Ya Ɗora Wa Yaƙin Rasha Da Ukraniya Laifin Matsalar Najeriya:
Shugaba Buhari a cikin wasiƙar ya ɗora laifin wannan matsalar a kan yaƙin Rasha da Ukraniya da kuma ‘yan-ta-more masu satar ɗanyen mai da fasa bututun mai. Ya ce su ne suka haifar da kai adadin kuɗin tallafin mai na shekarar 2022 zuwa naira tiriliyan 4.
“Tashin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, wanda yaƙin Rasha da Ukraniya ya haddasa ne ya haifar da ƙarin adadin kuɗaɗen tallafi zuwa naira tiriliyan 4. Sai kuma ɓarnar da masu satar ɗanyen mai ke yi ta sa tilas za a rage yawan wanda ake haƙowa.” Inji Buhari.
Idan ba a manta ba, Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin cire tallafin mai a cikin watan Janairu, 2022. Sai dai kuma barazanar tafiya zanga-zangar sai-Baba-ta-gani da gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago suka yi, ta sa gwamnati ta fasa cire tallafin mai ɗin.
Dama kuma Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ta yi bayanin cewa Gwamnatin Tarayya za ta kashe naira tiriliyan 3 wajen biyan kuɗaɗen tallafin mai a shekarar 2022.
Yaƙin Rasha da Ukraniya ya ƙara tsadar ɗanyen mai a duniya. Sannan kuma yaƙin ya ƙara wa tataccen fetur farashi a kasuwannin duniya. Haka kuma kuɗin dako da kuɗin lodi da kuɗin saukale daga Turai zuwa Najeriya duk sun ƙaru.
Har yau bayan shekaru bakwai da hawa mulkin Buhari, ya kasa cika alƙawarin gyara matatun mai na Kaduna, Warri, Legas da Fatakwal domin a riƙa tace fetur a Najeriya.
Gwamnatin Najeriya dai a farkon wannan shekarar ta ce ta dogara ne da ganin cewa an kammala gina Matatar Dangote domin a riƙa samun sauƙin sayen fetur a gida, ba sai daga ƙasashen waje ba.
Duk da matatun Najeriya ba su iya tace ko galan ɗaya, a duk shekara ana kashe masu biliyoyin nairori ko dai ta fuskar ƙoƙarin gyaran da a kullum ya ƙi yiwuwa, ko kuma ta fuskar iƙirarin kusa da matattun masana’antun tace man.