Hukumar ICPC ta bayyana yadda wasu uku a Kebbi, Jigawa da Taraba suka yi amfanin da ofis ɗin su, suka cuci talakawan yankunan da su ke wakilta, ta hanyar mayar da ayyukan jama’a zuwa na amfanin kan su.
ICPC ta bayyana yadda Sanatocin suka yi uwa-makarɓiyar shigewa gaba aka bayar da kwangilar ayyukan raya mazaɓu ga kamfanonin da ko dai na su ne, ko na ‘yan uwan su, ko na ‘ya’yan su da matan su, ko kuma wanda suke da jari a ciki.
Duk wannan fallasar ta na cikin wani gangariyar rahoton Bin Diddigin Ayyukan Raya Mazaɓu wanda ICPC ta gudanar, mai suna CEPTi.
Rahoton ya kuma gano yadda wasu kayayyakin da talakawa ne ya kamata su amfana da su, amma aka gan su a gidajen iyalai ko ‘yan uwan wasu Sanatocin.
Da farko ICPC a ƙarƙashin shirin Bin Diddigin Ayyukan Raya Mazaɓu (ZIP) da ake kira ‘Zonal Intervention Projects’, ta bi ayyuka 490 waɗanda aka yi walle-walle, sarambe da asarƙala da hankulan talakawa musu zaɓe.
ICPC ta gano cewa Sanatocin na haɗa baki da wasu jami’an Ma’aikatun Gwamantin Tarayya da Hukumomin Gwamnati.
Haka kuma an bankaɗo wani walle-walle ɗin da aka binciki Ayyukan Raya Mazaɓu 232 da aka yi tsakanin Yuni 2020.
Premium Times ta samu kwafen Ayyukan Raya Mazaɓu 722 da aka bi diddigin su, waɗanda aka yi iƙirarin an yi tsakanin 2015 zuwa 2020. Kuma ayyukan duk an saka su a cikin Kasafin Shekarun 2015 zuwa 2020 ɗin a cikin jihohi 16.
Kowane aikin kamar yadda ICPC ta bankaɗo, ya haura kwangilar Naira miliyan 100 abin da ya yi sama.
Ayyukan Naira Tiriliyan 2 Sun Tafi A Banza Tsakanin 2000 zuwa 2020 -ICPC:
Hukumar ICPC ta ce aƙalla an kashe naira tiriliyan 2 daga 2000 zuwa 2020 da sunan ayyakan raya mazaɓu ta hannun Sanatoci da ‘Yan Majalisa.
Sai dai kuma duk inda ka kewaya a ƙasar, kowane yanki jama’a kuka su ke yi a kan yadda ake gudanar da wasu ayyukan jigari-jigari, wasu a fara ba a ƙarasa ba, sai a yi watsi da ayyukan, ko kuma ma a karkatar da kuɗin ba tare da an yi aikin ba. Amma kuma a takarda ga katafaren aikin nan a rubuce an yi, an kuma kwashe kuɗaɗen.
Aliero, Sabo Nakudu Da Bwacha: Samfurin Sanatocin Da ICPC Ta Zaɓule Wa Tazuge A Tsakiyar Kasuwa:
Waɗannan sanatoci ne waɗanda su ka shiga suka fita, aka bada ayyukan kwangilar wasu ayyuka da kamfanonin su ko na ‘ya’yan su da matan su.
Ayyukan sun haɗa har da samar da motoci, ɗimbin injin samar da ruwa da gine-gine da sauran su a Mazaɓar Kebbi Ta Tsakiya, Jigawa Kudu maso Yamma da Taraba Ta Kudu.
Sanatocin su ne Adamu Aliero na KEBBI, Sabo Nakudu na Jigawa da kuma Emmo Bwacha na Taraba.
Adamu Aliero:
Hukumar ICPC ta kama Sanata Aliero da laifin bayar da kwangila ga kamfanin da mallakar ‘ya’yan sa ne. Kwangila ce samar da injinan samar da ruwan famfo a Mazaɓar sa ta Kebbi ta Tsakiya. Sunan kamfanin Voltricity Nig. Ltd.
“ICPC ta gano cewa Aliero wanda ya yi Gwamna a jihar Kebbi tsakanin 1999 zuwa 2007, yanzu da ya ke Sanata ya sa an bayar da kwangilar ce ga kamfani mallakar ‘ya’yan sa.”
An kuma gano cewa wasu kamfanoni uku kacal sun gudanar da ayyukan kwangiloli a Mazaɓar Sanata Aliero, waɗanda su ka haɗa da Alliance Trading Co. Ltd, Hummingbird Projects and Services da kuma Puranova Nig. Ltd. Dukkan waɗannan kamfanoni na ‘ya’yan Aliero ne na cikin sa.
“ICPC ta kuma ƙwato sama da injinan bayar da ruwan famfo 1,000 an ɓoye a wasu gidaje, su na ɓoye tun 2019 ba a raba su talakawa sun amfana ba.
Sanata Emmanual Bwacha:
Shi ne Sanata mai wakiltar Taraba ta Kudu. Shi ma kwangilar gyaran gine-ginen ajujuwa a Makarantar ‘Ya’yan Malaman Jami’ar Tarayya ta Wukari ya bayar ga kamfanin sa.
ICPC ta ce Bwacha ya bayar da kwangilar a kamfanin Eloheem Educational Management and Schools Ltd, da na sa ne, halak-malak’.
“Sanata Bwacha ya damfari gwamnatin tarayya ya sa ta zuba kuɗi ga wani aiki na sa na ƙashin kan sa, na gina sakandare a Jami’ar Tarayya ta Wukari, a matsayin aikin mazaɓar sa.
Haka kuma ICPC ta ce Sanata Bwacha ya karkatar da kwangilar samar da injinan ruwa na mazaɓar sa.
“Kwana biyu bayan an bayar da Kwangilar ga S.A Kadiri Ltd, sai kamfanin ya rubuta wasiƙa ga Hukumar Lower River Benuwai Basin Development Authority, cewa yanzu kamfanin Eloheem Ltd ne zai yi kwangilar. Eloheem Ltd kuwa mallakar Sanata Emmanual Bwacha ne.
Rahoton ya ci gaba da bankaɗo daƙa-daƙa da karkatar da ɗimbin kayayyakin da haƙƙin talakawa ne da Bwacha ya riƙa yi.
Sanata Sabo Nakudu, Jigawa:
ICPC ta kama Sabo Nakudu da laifin bayar da kwangilar gina rijiyoyin burtsate, samar da famfuna, babura, mota samfurin Toyota Hilux da sauran su ga kamfanin da mallakar ƙannen sa ne.
Sunan kamfanin Schramn Global Services Ltd. Tun 2016 aka bayar da kwangilar samar da motocin, amma na a kai ba. Daga baya ICPC ta kama motocin a hannun wani ƙanin Nakudu.
PREMIUM TIMES ta yi ƙoƙarin jin ta bakin sanatocin, amma abin ya faskara