Sanata Uba Sani dake wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya yi wa mutan Kaduna goma ta arziki inda ya yi wa talakawa ambaliyar abincin azumi da na sallah dake tafe a faɗin jihar.
Sanata Uba ya raba wa talakawa buhunan abinci da suka haɗa da shinkafa, sikari, Indomie taliya da ɗan kudin cefane ga marasa karfi a faɗin jihar.
Da yawa daga ciki waɗanda suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA sun shaida cewa wannan kyauta ya zu akan gaɓa ne.
” Kowa ya san halin da ake ciki yanzu, matsin ya kai maƙura amma kuma sai gashi ya yayyafa mana ruwan sanyi ta hanyar raba mana abinci domin mu da iyalan mu.
” Wani abu da zai birgeka shine ba kawai tsukin yankin da yake wakilta bane ya rabawa abinci kaf gaba ɗaya ƙananan hukumomin jihar Kaduna ne 23 ya rabawa abinci. Talakawa sun yi matuƙar farin ciki da wannan abu.” Inji Hamza Atiku mazaunin karamar hukumar Ikara.
Agnes Wada, ta bayyana cewa ba tun yanzu bane sanatan yake kula da mutane a jihar Kaduna.
” Ga shi dai a cikin azumi ne ya yi rabon amma ba musulmai bane kawai aka aika wa abinci harda waɗanda ba musulmai ba. Wannan shine abinda muka saba daga wurin sanata Uba. Kowa ne nashi, baya zaɓar wasu ya bar wasu.
Sanata Uba na daga cikin ƴan takaran da ke kan gaba wajen maye gwamna El-Rufai a 2023 idan wa’adin mulkinsa ya cika.
Soyayyarsa ya game jihar inda da dama ke cigaba da lunƙuya cikin tafiyar sanatan babu ƙaƙƙautawa a jihar.