Sanata Uba Sani dake wakiltar Kaduna Ta tsakiya a majalisar Dattawa ya bayyana cewa majalisar ta gargadi manyan hafsoshin tsaron Najeriya da ja musu kunne su maida hankali wajen samar da tsaro a fadin kasar nan, musamman yankin Arewa Maso Yamma.
Sanata Uba ya ce tabbas tura fa ta kai bango domin ‘yan bindiga sun samu daman cin karen su ba babbaka saboda sakaci da aka samu a wasu sassan tsaron kasar nan.
” Yanzu sai ka tashi tun daga Abuja zuwa Kaduna ko kuma Kaduna zuwa Abuja, ka kuma yi tafiyar fiye da kilomita daya baka ci karo da wani jami’in tsaro dake aiki a wannan hanya ba wanda kuma ba haka yakamata ba idan har tsaron ake so a samar wa talakawa.
” Yana daga cikin kira da muka yi wa manyan hafsoshin tsaron kasar nan da su yi amfani da karfin soja da suke da shi domin kawo karshen wannan matsala ta tsaro a musamman yankin Arewa Maso Yamma da kasa baki daya.
” Majalisa na ware wa fannin tsaro makudan kudade domin su yi amfani da su. Su je su dibi wadannan kudade su tunkari wadannan mahara domin gamawa da su. su yi musuluguden bama-bamai a wuararen da suke boye.
Yankin kaduna ta Arewa na daga cikin yankunan da ke fama da matsanancin rashin tsaro a jihar Kaduna. Karamar Hukumar Giwa, birnin Gwari, kajuru da Chikun duk suna fama da harin yan bindiga.
Cikin hubbasan da yake yi shine gaggauta sanar da majalisa halin da mutanen sa ke ci a jihar domin a samar musu da mafita ta hanyar yin dokoki da tilasta jami’an tsaro su kai tsaro wannan yankuna.
Bayan haka wajen kula da mutanen sa, sanata uba bai yi kasa a guiwa inda yakan gaggauta kai musu dauki na tallafin domin kwantar musu da hankali a koda yaushe.
Discussion about this post