Hukumar babban birnin tarayya Abuja ta garkame wasu ma’aikatu a Abuja a dalilin tulin bashi da take binsu.
Hukumar AEPB ta garƙame ma’aikatun ranar Talata saboda tulin bashin naira biliyan 10 da take bin ma’aikatun na haraji da sauransu.
Ma’aikatu da hukumomin da aka garƙame sun hada da ma’aikatar aiyukka da gidaje na gwamnatin tarayya dake Mabushi, ma’aikatar tsaro, ma’aikatar lafiya na tarayya, Hukumar muhalli, Ma’aikatar kasuwanci da Zuba Jari ta Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Tsaro ta Civil Defence a Wuse, da dai sauransu.
Kafin ya kai ga haka hukumar ta Kai wadannan ma’aikatu Kara a kotun majistare dake Wuse Zone 2 inda kotun ta umurci ma’aikatun da su bayyana a kotun ranar 30 ga Maris amma suka ki zuwa.
Shugaban hukumar AEPB, Osilama Braimah Wanda ya jagoranci jami’an tsaron da suka garƙame wadannan ma’aikatu ya sanar da haka.
Braimah ya ce hukumar na bin ma’aikatar aiyukka da gidaje N9,998,625.00, ma’aikatar tsaro naira N17,220,775.00, hukumar gyara Hali ta naira N10,128,906.25, hukumar tsaro na civil defence 2,451,649.50, hukumar yara haraji 21,683,750.00.
Saura sun hada da ma’aikatar lafiya N14,204,843.75, ma’aikatar kasuwanci da zuba jari N19,222,287.50 ma’aikatar ilimi N25,838,275.
Braimah ya ce hukumar AEPB ta yi kokarin a sasanta da wadannan ma’aikatu amma suka ki.
“A dalilin haka ya sa hukumar ta nemi izini wurin kotu domin ta garkame ma’aikatun.
Ya ce yin haka na daga cikin aiyukkan da hukumar za ta rika yi wa sauran ma’aikatun gwamnati da wadanda ke zaman kansu da suka ki biyan su bashin kudaden su.