Kayan abinci da kayan masarufi sun tsawwala tsadar da ƙure aljihun mai ƙaramin ƙarfi, yayin da ‘yan ya-mu-samu ya-mu-sa-bakin-mu ke gaganiyar neman abinci a tsawon rayuwar su ta duniya.
Wannan tsadar rayuwa ta kayan abinci ta yi masifar tashi a cikin watan Maris, sanadiyyar ɓarkewar yaƙin Rasha da Ukraniya.
Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) ta ce kayan abinci sun yi tsadar da ba su taɓa yi ba a cikin watan Maris.
Man girki da akamun gwangwani samfurin seralak da nama su ma duk farashin su ya yi sama, kamar yadda ƙididdigar da FAO ta fitar a ranar Juma’a ta nuna.
Rahoton ya bayyana yadda kayan abincin da ba a kai ga dafawa ko sarrafawa ba ya ƙara farashi sosai a faɗin duniya.
Idan aka auna da farashin cikin watan Fabrairu, za a ga cewa a cikin Maris farashin ya ƙaru da kashi 17.9, saurin tashin farashin tun cikin 1990 ba a sake gani ko fuskantar irin sa cikin ƙanƙanin lokaci ba, sai a Maris na watan jiya.
Kayayyaki irin su sugar da madara ta ruwa da ta gari, duk sun ƙara kuɗi, kamar yadda rahoton FAO ya tabbatar.
A Najeriya dai farashin man gyaɗa ya tashi, “haka a duniya duk wani nau’in man girki ya ƙara tsada a cikin Maris.”
“Saboda wasu kayan tilas sai an bi ta tekun ‘Black Sea’ da su, ruwan da a yanzu ya zama lahira kusa, saboda gumirzun yaƙin Rasha da Ukraniya da ake yi a yankin.”
FAO ta ƙara da cewa shi ma farashin man ja da na man waken soya ta yi tashin-gwauron-zabo, saboda neman su da ake yi wurjanjan, dalilin ƙarancin sauran nau’ukan man da safarar su ba ta yiwuwa zuwa wasu ƙasashen duniya, saboda yaƙin Rasha da Ukraniya.
Bayan waɗannan kuma, farashin alkama da nau’ukan su shinkafa da hatsi duk ya tashi a duniya, kuma babban dalilin hakan shi ne yaƙin Rasha da Ukraniya, wanda ya hana jiragen ruwa gangancin giftawa ta ruwan.
“Kasa gudanar da safarar alkama ta cikin ‘Black Sea’ ya haifar da ƙarancin ta da ƙarin farashin ta a duniya.
Alkama na da muhimmanci a duniya, saboda yadda ake sarrafa ta ana samar da abinci kala-kala a duniya.
Farashin alkama a cikin watan Maris ya ƙaru da kashi 19.7 a duniya daidai lokacin da yawancin manoman alkama a Amurka ba su samu albarkar noma sosai a kakar da ta gabata ba.
Kayan gona irin su masara, gero da dawa sun yi ƙarin kashi 20.4 a cikin Maris, masifar tsadar da tun 1990 ba su taɓa yin irin ta ba.”
“Masara ta ƙara tsada da kashi 19.1, saboda Ukraniya ta daina fitar da masara a ƙasashen duniya. Kasancewar Ukraniya ƙasa da ke cikin sahun gaban ƙasashen da suka fi noman masara a duniya, yaƙi ya sa sun dakatar da sayar da masara a waje. Hakan ya sa ta ƙara tsada a duniya.”
“Yayin da Turai naman alade ya ƙara tsada, a saurwn manyan ƙasashen kuma naman kaji ne ya tsula masifar tsada, saboda dakatar da safarar sa daga wasu ƙasashe, saboda ɓullar cutar murar tsuntsaye. Sannan kuma an kasa samun naman kaji daga Ukraniya.
Ba a nan lamarin ya tsaya ba. Tsadar ta shafi naman shanu, ta yadda ƙasashen da ke dogara da sai an shigar masu da naman shanu daga waje, a cikin Maris zuwa yanzu su ke sayen sa da masifar tsada.
Idan mu ka dawo Najeriya, FAO ta ce ‘yan Najeriya kimanin miliyan 19.4 za su fuskanci yunwa da barazanar rashin abinci a cikin Agusta, 2022.
Wannan mumnunan labari ya zo daidai lokacin da ƙasaitaccen attajiri Aliko Ɗangote ya ce “a tashi a yi tanadin kayan abinci, domin yaƙin Rasha da Ukraniya zai haddasa ƙarancin abinci a duniya.”
Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cewa aƙalla ‘yan Najeriya miliyan 19.4 ne za su yi fama da yunwa da barazanar rashin abinci tsakanin watannin Yuni zuwa Agusta, 2022.
Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) ta yi wannan bincike tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Gona ta Tarayya da wasu Cibiyoyi masu ruwa da tsaki a harkar noma.
Rahoton ya yi nazarin matsalar ƙarancin abincin da za a fuskanta da kuma rashin abinci mai gina jiki a yankunan Sahel da Afrika ta Yamma.
Rahoton ya ƙara da cewa matsalar abinci za ta fuskanci aƙalla jihohi 21 na Najeriya tare da yankin Gundumar FCT Abuja, mai ƙananan hukumomi shida.
An kuma yi kirdadon aƙalla ‘yan gudun hijira 416,000 ne za su tsinci kan su cikin wannan mawuyacin halin tasku.
Sannan kuma rahoton ya nuna a yanzu haka aƙalla mutum miliyan 14.4 da kuma masu gudun hijira 385,000 sun afka cikin wannan halin rigimar gaganiyar ƙarancin abinci, kuma ba za su iya samun kan su a saiti ba, har sai cikin Mayu, 2022.
Jihohin da aka yi nazari a cikin Maris sun haɗa da Abiya, Adamawa, Benuwai, Barno, Cross Riba, Edo, Enugu, Gombe, Kaduna, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, Legas, Neja, Filato, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara, dai kuma Gundumar FCT Abuja.
A cikin shekarar da ta gabata dai FAO ta ce aƙalla mutum miliyan 12.8 na ‘yan Najeriya su ka yi fama da fari na ƙarancin ruwan shuka tsakanin Yuni zuwa Agusta, 2021.
Matsalar tsaron da ta dabaibayi samuwar abinci sun haɗa da yaƙin Boko Haram a Barno, Adamawa da Yobe, sai kuma hare-haren ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma, a jihohin Sokoto, Katsina, Zamfara, Kaduna da Kebbi. Sai kuma wasu jihohin Arewa ta Tsakiya da suka haɗa da Neja da Benuwai, waɗanda rahoton ya ce su ne lamarin zai fi yi wa riƙon laya a hannun ɗan dambe.
Sannan kuma rahoton ya ce matsalar tsadar kayan abinci da ya haddasa ƙuncin rayuwa a yanzu, zai ƙara ruruta wutar ƙarancin abincin sosai.
Sauran Matsalolin Da Ke Kara Ruruta Ƙuncin Rayuwa Da Rashin Abinci:
“Rashin aikin yi da suɓucewar aikin da mutum ke yi da kuma taguwar kuɗaɗen da magidanci ke samu sakamakon ɓarkewar korona, sai kuma fatattakar da ‘yan bindiga ke wa mutanen ƙauyuka da garuruwa su na yin hijira su zai ƙara kuma ya na ƙara munin matsalolin sosai.”
“Sauran dalilan da su ka sa matsalar ta 2022 za ta zarce ta 2021, shi ne saboda rashin hanyar isa wurin wasu masu gudun hijira da ke cikin lungunan Barno da Yobe, ƙarin munin hare-haren ‘yan bindiga da kuma ƙarin jihohi biyar da aka samu a cikin 2022.” Inji rahoton.
Wakilin Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) a Najeriya, Fred Kateero, ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya su yi amfani da sakamakon rahoton nan su shata wani tsari na ƙasa bai ɗaya, wanda zai bijiro da hanyoyin zabura a ceto harkar noma nan ba da daɗewa ba.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta zuba kuɗi sosai wajen tabbatar da samun nasarar wannan shiri.
Discussion about this post