Al’ummar garin Tsafe cikin Jihar Zamfara ta afka cikin tashin hankali a ranar Lahadi da dare, lokacin da wasu muggan ‘yan bindiga suka afka cikin garin, su ka buɗe wuta daidai lokacin da tsakiyar Sallar Tarawi da dare.
Majiya ƙwaƙƙwara ta ce an kashe mutane da yawa. Daga cikin waɗanda aka kashe, har da ɗan Kwamishinan Harkokin Tsaro na Jihar Zamfara, Mamman Tsafe.
Duk da dai gwamnatin Jihar ko Mamman Tsafe bai sanar da tabbacin kisan ɗan na sa ba, amma dai majiyoyi da dama sun tabbatar wa wakilin na mu kisan da kuma mummunan harin, wanda aka kai a unguwar Hayin Tumbi, kusa da gidan Kwamishinan Harkokin Tsaro.
Tsafe nan ne hedikwatar Ƙaramar Hukumar Tsafe, kuma ta na kan hanyar zuwa Gusau daga Funtuwa.
Wakilin mu ya ji cewa mutane da dama sun tsere daga garin yayin da su ka riƙa jin ƙarar bindigu na tashi babu ƙaƙƙautawa.
Wakilin mu ya tuntuɓi Kakakin ‘Yan Sandan Zamfara, ya ƙi yin ƙarin bayani. Amma ya ce za a fitar da sanarwa a ranar Litinin.
Zamfara na fatan da dandazon ‘yan bindiga waɗanda su ka hana kusan jihar baki ɗaya zaman lafiya.
Riƙaƙƙun ‘yan bindiga irin su Bello Turji, Yellow Ɗanbokolo, Auta Bubayi duk haifaffun cikin jihar Zamfara ne.