Shugaban NNPC Mele Kyari ya tabbatar da gaskiyar iƙirarin da Shugaban Bankin UBA, Tony Elumelu ya yi cewa ɓarayi ke sace kashi 95 bisa 100 na ilahirin ɗanyen man da ake loɗi a Tashar Jiragen Ruwa ta ‘Bonny Terminal’, Jihar Ribas.
Idan ba a manta ba, a ranar 17 Ga Maris ne Elumelu ya wallafa a shafin sa na Tiwita cewa “kashi 95 bisa 100 na ɗanyen man da ake haƙowa a Tashar Bonny Terminal, duk sace shi ake yi, lamarin da ya kai har kamfanin Shell ya daina haƙo ɗanyen mai a wurin.
“Ku dubi dai Tashar Lodin Mai ta ‘Bonny Terminal’, wadda kamata ya yi a ce a kullum ta na sauke ganga 200,000. Amma wanda ake saukewa bai fi ganga 3000 a kullum ba.
Haka Elumelu ya rubuta a shafin sa na Tiwita.
Iƙirarin da Elumelu ya yi ya tabbata gaskiya, domin Shugaban NNPC Mele Kyari ya tabbatar da cewa ganga 3,000 kaɗai ake turawa daga Bonny Terminal’, daga cikin ganga 293,000 da ake haƙowa.
Kyari ya yi wannan bayani a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya. Ya ƙara da cewa an sace ɗanyen mai na aƙalla dala miliyan 4 ga ɓarayin mai a kullum.
Ya ce aƙalla a ana sace ganga 200,000 ta ɗanyen mai a kullum a cikin 2021.
Ya ce Najeriya ta yi asarar dala biliyan 1.5 a cikin 2022.
“Abin da ke faruwa shi ne masu fasa bututu ke sace ɗanyen mai suka sa muka yi asarar ɗanyen mai mai tarin yawa. Sannan kuma lamarin ya haifar da dakatar da haƙo ɗanyen mai a wurin.
Ya ce an rufe rijiyoyin haƙo ɗanyen mai biyu, saboda ɓarayin ɗanyen mai.
Sannan Kyari ya ce ɓarayin da ke sace fetur ɗin ƙwararru ne ƙwarai, ba ‘yan dagaji ba ne.
Daga nan ya roƙi Majalisa ta bai wa Gwamnatin wa’adin watanni biyu domin ta fara aiki da tsare-tsaren matakan tsaron da ta ɗauka waɗanda za su kawo ƙarshen satar mai da fasa bututun mai a yankin Neja Delta.
Ɗan Majalisa Sergius Ogun, ɗan PDP daga Ogun, ya karanto amincewa da buƙatar bai wa NNPC wa’adin watanni biyu ɗin.
Daga nan kuma kwamitin ya shiga ɗakin taron sirri, wanda ba a yarda manema labarai su shiga ba.
Idan ba a manta ba, shi ma Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa Majalisar Tarayya cewa matsalar ɓarayin mai da masu fasa bututu ya kawo cikas da dakatar da haƙo wani kaso na ɗanyen mai a Najeriya.