Ministan Sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Ribas Rotimi Amaechi ya bayyana cewa shima zai yi takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC a 2023.
Amaechi ya bi sahun tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, Richas Okorocha, gwamna David Umahi, Sanata Orji Kalu da kuma wasu da ake raɗe-raɗin nan ba da dadewa ba za su bayyana niyyar fitowa takarar a jam’iyyar.
A jawabin da yayi a wajen kaddamar da takarar shugaban kasa da yayi, Amaechi ya ce ” Dalilin da ya sa ya fito takarar shine domin ya dawowa Najeriya da martabarta da ta rasa a dalilin matsalolin da kasar ta faɗa ciki.
” Yanzu Najeriya na cikin halin ha’ulai musamman a harkar tsaro da ya ki ci yaki cinyewa, sannan kuma ga matsalar rashin aikin yi ga matasa da kuma rugujewar tattalin arziki. Waɗannan suna dalilan da ya sa naga ya dace in fito takarar domin mu gyara kasar.
” Waɗannan matsaloli ba a Najeriya ba kaɗai duk duniya an faɗa cikin matsaloli irin haka.
” Shekaru na 23 ana fafatawa da ni a harkar siyasar ƙasar nan. Tun daga karanar hukuma zuwa majalisa, gwamna da mutane nisra da nake kai yanzu. Na san abinda ya dace ayi don cigaban kasa.
Idan ba a manta ba shima abokin hamayyarsa wanda ba su ga maciji, gwamnan Ribas, Nysome Wike ya fito takarar a jam’iyyar PDP.