Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Adamu ya yi karin haske kan saka naira miliyan 100 kudin fom din takarar shugaban kasa.
Adamu ya Yi wannan ƙarin haske ne lokacin da yake yin hira da VOA Hausa.
Ya ce maganar shugabancin ƙasa ba na sarkin gari ba ” domin idan sarkin garin ku ya mutu masu neman sarauta kan kashe fiye da naira miliyan 100.
” Baya ga haka akwai abubuwa da dama da idan mutum na nema a kasar nan sai ya sa fiye da naira miliyan 100 kafin a yi da shi.
Kuma idan mutum da gaske yake ya shiga zaben shugaban Najeriya idan ba shi da hanya bashi da masoyan da za su haɗa masa miliyan 100, bai cancanci ya shiga zaben shugaban Najeriya ba.
” A Amurka sanin ka ne idan mutum zai nemi shugabancin ƙasar koda fakiri ne bai da komai masu son shi suna iya hada kai su bi jiha-jiha su tara kudin da suke bukata don su biya. Wannan dokar nasu ya yi haka.
Mai neman miliyan 100 za ka ga ya samu miliyan barkatai ta hanyar gudummawa daga masoyan sa.
Shugaban Najeriya ba wasa bane sannan ba ana neman sarkin tashan garin ku bane shugaban Najeriya ne saboda haka dole mai so sai ya shirya sosai.
Me ya haɗa batun shugabancin Najeriya da cin hanci da rashawa?
Idan za ka shiga ka shiga ba dole.
Ko ina a duniya ka gaya mun ƙasa daya da basu biyan kudin jam’iyya ba in dai kasar demokradiyya ta ke yi.
Wannan nema ake a ɓata mana suna kawai Kuma abokan adawar mu ne kuma hakan ba shine zai sa mu tsaya ko mu canja ba.
Duk wanda zai shiga zaben shugaban ƙasa a tutar jami’ar mu abin da zai biya kenan.
Discussion about this post