Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya bayyana a fili neman takarar shugaban ƙasa a 2023.
Osinbajo ya nuna aniyar sa ta son hawa shugabancin ƙasa bayan saukar Shugaba Muhammadu Buhari a Mayu, 2023.
Ɗan asalin Jihar Ogun, Osinbajo ya yi Kwamishinan Shari’a na Jihar Legas a lokacin mulkin Bola Tinubu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ƙaddamar da neman fitowar sa takara a shafin sa na Facebook, a safiyar Litinin ɗin nan.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Osinbajo zai bayyana buƙatar fitowar sa takarar shugaban ƙasa a ranar Litinin.
A yau Litinin ne zai yi ganawar buɗa-baki da gwamnonin APC Musulmi a gidan sa, inda zai shaida masu fitowar sa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023. Duk da dai dama majiyar mu ta tabbatar mana cewa ya bi su ɗaya bayan ɗaya ya shaida masu.
Osinbajo ya ce a shekaru bakwai da ya yi ya na mataimakin ɗan kishin ƙasa Shugaba Buhari, ya kewaya ƙasar nan baki ɗaya. Kuma ya gana da ƙabilu daban-daban, tare da jin koken yankuna da ɓangarori daban-daban.
“A tsawon shekaru bakwai ina Mataimakin Shugaban Ƙasa mai kishi, Muhammadu Buhari, na samu damar kewaya ƙasar nan sosai, kuma na gana da jama’a da ƙabilu. Na saurari bayanai da koke-koken su.
“Na tsaya tare da jama’a, na zauna tare da su kuma fahimci halin da su ke ciki da damuwar su.
“Dalili kenan a yau na fito ina mai ƙasƙantar da kai a gaban ku, tare da bayyana aniya ta ta neman tsayawa takara a zaɓen 2023 na zaɓen shugaban ƙasa. Zan tsaya ne a ƙarƙashin jam’iyyar mu mai albarka, APC.
“Ina neman goyon bayan ku. A yanzu lokacin fitowar tawa ce ya yi.”
Osinbajo zai fatata da irin su ubangidan sa Bola Tinubu, Rotimi Amaechi, Rochas Okorocha da wasu masu neman tsayawa takarar a ƙarƙashin APC.
Tuni dai Osinbajo ya buɗe ofishin kamfen a Abuja, kuma aka buɗe shafin jin ra’ayin jama’a a intanet.