Akalla mutum 97 ne ‘yan bindiga suka kashe a makon da ya gabata a Najeriya, daga ranar 27 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu.
Alkaluman yawan mutanen da aka kashe a kasar nan a makon da ya gabata ya Kara tabbatar da yadda tsaro ya tabarbare a kasar.
Daga cikin mutum 97 din da aka kashe mutum shida sojoji, 91 farin hula.
‘Yan bindigan da suke kai wa mutane hari a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya sune suka kai hari na akalla kashi 50% daga cikin hare-haren da aka Yi a cikin makon.
Kaduna
‘Yan bindiga sun kashe mutum 15 a kauyen Yayin Kanwa dake karamar hukumar Giwa.
Wani mazaunin kauyen Mohammed Buwala ya bayyana cewa an yi jana’izar waɗanda suka rasu ranar Litinin da ya gabata.
Daga nan ‘yan bindiga sun kashe mutum 8 kuma sun yi garkuwa da mutane da dama a harin da suka yi a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
Zamfara
A ranar Talatan makon jiya ‘yan bindiga sun kashe mutum hudu a kananan hukumomin Talata Mafara da Bakura.
Ƴan bindigan sun kashe wadannan mutane a kauyukan Ruwan Gora da Ruwan Gizo dake karamar hukumar Talata Mafara da Yar geda dake karamar hukumar Bakura.
Bayan haka tsakanin ranakun Alhamis da Juma’a ‘yan bindiga sun kashe mutum 35 a kauyuka biyar dake karamar hukumar Anka.
Majiya daga kauyukan sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun saci dabbobi da dama.
Enugu
Akalla mutum daya ya mutum sannan wasu mutum biyu sun ji rauni a dalilin harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Odegba dake karamar hukumar Enugu ta Arewa a jihar Enugu.
Anambra
Mutum daya ya mutu bayan ‘yan bindiga sun afka hedikwatar karamar hukumar Nnewi ta Kudu dake kauyen Ukpor a jihar Anambra.
Majiya ta ce ‘yan bindigan sun kai mutum 50 da suka Kai wa hedikwatar hari.
Ogun
Mutum 16 ne suka rasa rayukansu a rikicin da aka yi tsakanin kungiyoyin asiri na Eiye da Aiye dake Sagamu a jihar Ogun.
An Kuma Kara samun gawarwakin mutane bayan mahara sun kashe mutum bakwai a wasu yankunan Abeokuta.
Filato
‘Yan bindiga sun kashe mutum biyar sannan wasu mutum uku sun ji rauni a harin da aka kai a kauyen Iregwe dake karamar humumar Bassa jihar Filato.
Kakakin kungiyar samar da ci gaba na Iregwe Davidson Malison ya ce tuni sun sanar wa ‘yan sanda da sojoji.
Neja
‘Yan bindiga sun kashe Sojoji shida a Suleja a daren Litinin da ta gabata.
Benue
A ranar Talatan da ya gabata ‘yan bindiga sun kashe mutum hudu a karamar hukumar Guma, Kwande da Gwer ta Yamma a jihar Benuwai.
Gwamnan jihar Samuel Ortom ya sanar da haka.
Ebonyi
Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum biyu a karamar hukumar Ikwo.
Kakakin rundunar Loveth Odah wacce ta sanar da haka ranar Asabar ta ce maharan sun far wa kauyen ne a ranar Juma’a.