Akalla mutum 35 ne ‘yan bindiga suka kashe a kauyuka biyar dake karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.
‘Yan bindigan sun far wa kauyukan a ranakun Alhamis da Juma’a inda har dabbobi suka sace daga waɗannan kauyuka.
Kauyukan da ‘yan bindigan suka afka wa sun hada da Kadaddaba, Rafin Gero, Babban Baye, Wanu da Daki Takwas.
Shugaban matasa a kauyen Wanu Shawwal Aliyu ya ce dagacen kauyen na daga cikin mutanen da ‘yan bindigan suka kashe.
“Da ‘yan bindigan suka shiga kauyen sai suka wuce zuwa gidan dagacen inda a nan suka iske mutanen da suka zo neman mafaka a gidan suka harbe su.
Aliyu ya ce ‘yan bindigan sun kashe mutum shida a Wanu, mutum hudu a Kadaddaba, biyu a Babban Baye da uku a Rafin Gero.
“A ranar Alhamis wadanda suka tsira da ran su sun gudu zuwa Anka inda a nan ma ‘yan bindigan sun kashe mutum 15 duk da cewa mutane sun yi ta kiran jami’an tsaro.
PREMIUM TIMES ta samu bayanin cewa ‘yan gudun hijira na zama a filin makarantar firamare da wani fili da sarkin Anka ya bada.
A ranar Juma’a ‘yan bindiga sun kashe mutum 20 a Daki Takwas.
Daki Takwas kauye ce dake kusa da cikin gari da Kwalejin Anka dake mallakin gwamnatin tarayya.
Wani mazaunin kauyen Ansar Aliyu ya ce ‘yan bindigan sun shigs kauyen a daidai mutane na shirin zuwa kasuwar Anka da safe inda a nan suka harbe mutum 20.