Majalisar zartaswa ta Kasa ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu 12 a faɗin kasar nan.
Ministan yaɗa labarai, Lai Mohammed ne ya faɗi haka da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnatin tarayya.
Jami’o’in sun haɗa da Pen Resource University Gombe, Jihar Gombe, Al-Ansar University, Maiduguri, jihar Borno, Margaret Lawrence I -University, jihar Delta, Khalifa Ishaku Rabiu University Kano, jihar Kano.
Sports University Idumuje Ugboko, jihar Delta, Bala Ahmed University Kano, Saisa University of Medical Sciences and Technology, Sokoto State, Nigerian-British University Hasa, iihar Abia, Peter University Acina-Onene, jihar Anambra, Newgate University, Minna, jihar Niger, European University of Nigeria in Duboyi, Abuja da North-West University Sokoto. ”