Wasu daga cikin ƴan gaban goshin shugaban Kasa Muhammadu Buhari har yanzu basu ce komai ba game da yafe wa wasu gwamnoni da Buhari yayi bayan an kama su da laifin handame kuɗaden talakawan jihohin su.
Idan ba a manta ba, a cikin makon jiya shigaban kasa Buhari ya yafe wa tsoffin gwamnonin jihohin Taraba, Jolly Nyame da Joshua Dariye na Jihar Filato, wanda aka ɗaure bayan an kama su da laifin handame kuɗaden talakawan jihohin su
Bayan sallamar su da gwamnati ta yi, mutane da dama harda wasu jami’an hukumar EFCC da na ICPC sun nuna rashin jin daɗinsu akan abinda shugaba Buhari yayi.
Kafin nan jama’a na korafin tunda a baya, makusantan shugaba Buhari wato na kud da kud ɗin sa sun rika yin suka ga gwamnatin Jonathan a lokacin da ya yafe wa tsohon gwamnan jihar jihar Bayelsa da ke ɗaure a lokacin bayan an kama shi da laifin yin sama da faɗi da kuɗaden jama’a, ya kamata yanzu su fito su maimaita abinda suka yi a baya.
” Ya kamata mutane irin su gwamna Nasir El-Rufai da minista Festus Ketamo da suka rika kumfar baki, suna zazzaro idanu da jijiyoyin wuya a lokacin da Jonathan ya yafe wa Alamesigh, su fito yanzu su yi kururuwa a ji su.” In ji Adam Kasim, wani mai rajin kare hakkin Ɗan Adam.
Shi ma minista Keyamo ya sufafi Jonathan da gwamnatin sa, inda ya rika kiran gwmatin malalaciya wacce ta ɗaure wa cin hanci da rashawa gindi.
Ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba. Amma yanzu kwanaki biyar kenan da yafe wa waɗannan gwnoni da Buhari yayi amma basu ce tak ba.
Discussion about this post