Yayin da tuni aka fara yaƙin neman zaɓen fitowa takarar zaɓen fidda-gwani na masu fitowa takarar muƙamai daban-daban, duk har yanzu Hukumar Zaɓe ba ta bayar da umarnin fita kamfen ba.
Maganar da har yau ba ta jiƙu a bakunan mutane a fagen siyasa ba ko a fagen masu sharhin siyasa, ita ce waɗanda za su yi wa kowane ɗan takarar rufa bayan yi masu mataimakin shugaban ƙasa.
Sau da yawa dai ɗan takarar shugaban ƙasa ba ya fitar da mataimakin sa har sai bayan ya ci zaɓen fidda-gwani tukunna. Hakan kuwa kan kasance ne ko dai ya ɗauko wanda ya ke ganin zai tafi tare da shi a tsanake idan ya yi nasarar cin zaɓe, ko kuma ya kasance an yi yarjejeniya an ba shi mataimaki daga wani yankin da ake buƙatar ƙuri’ar su wurjanjan.
A zaɓen shugaban ƙasa na 2023 dai hankula za su fi karkata ne a kan ‘yan takarar APC da kuma PDP. Sai kuma Rabi’u Kwankwaso na NNDP.
To amma kafin a kai zaɓen, abin tambaya shi ne, su wa za su yi nasara a zaɓen fidda-gwani? Kuma su wa kowanen su zai ɗauka matsayin mataimakin shugaban ƙasa ne.
A cikin APC dai akwai manya kuma gaggan ‘yan takarar da suka haɗa da Bola Ahmed Tinubu, wanda tun farkon lokacin da ya nuna kwaɗayin mulkin sa aka riƙa raɗe-raɗin cewa zai ɗauki Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a takarar sa.
An riƙa ganin alamomin haka, ganin yadda Ganduje ke yawan shigewa gaba a al’amurran siyasar Tinubu.
Masu sharhi na ganin akwai matsala a ɓangaren Ganduje. Da dama na ganin cewa idan Tinubu ya tafi da Ganduje, to yarfen zargin cushen daloli da ake yi wa Ganduje zai yi tasiri sosai a bakunan ‘yan adawa, musamman PDP.
Ba mamaki dalili kenan wasu ke cewa Tinubu ka iya jingine tunanin ɗaukar Ganduje, ya ɗauki tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, wanda idan an yi haka, to alama ce ta ƙoƙarin jawo ƙuri’un Kiristocin Arewa su zaɓi APC.
Wani babban ɗan takarar shugaban ƙasa a APC shi ne Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo. Ana ganin ko kuma ji-ta-ji-tar cewa Osinbajo zai rungumi Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Duk da Zulum ya fito ya ce ba neman takarar shugaban ƙasa ko ta mataimaki ce a gaban sa ba, hakan ba zai hana ya karɓa idan an yi masa tayi.
Akwai kuma Ministan Harkokin Sufuri Rotimi Amaechi a cikin masu neman takara ƙarƙashin APC.
Ganin cewa Amaechi ya fito ne daga yankin Kudu maso Gabas, ana hasashen cewa idan Amaechi ya yi nasarar lashe zaɓen fidda gwani, to zai zaɓi Gwamna Nasir El-Rufai ne na Kaduna a matsayin mataimakin sa.
Akwai ‘yan takara da dama waɗanda har yanzu ba a kai ga yin hasashen tantance mataimakan da za su tsayar ba.
Sun haɗa da Rochas Okorocha, Emmanual Udom da wasu ɗaiɗaiku.
A PDP kuwa, yayin da ake hasashen cewa idan Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya yi nasara, to zai ɗauki Gwamna Nysom Wike na Ribas a matsayin mataimakin takarar sa.
Da ya ke shi ma Wike ɗin ya fito neman takara, idan shi ne ya yi nasara, to zai ɗauki Tambuwal ne a mataimakin sa.
Yayin da babu tabbas ko wani ingantaccen hasashe a ɓangaren wanda Anyim P. Anyim zai naɗa mataimakin sa a takara idan ya yi nasara a PDP, ana ganin wataƙila Bukola Saraki ya yi tunanin naɗa Anyim mataimakin sa, don PDP ta jawo ƙabilar Igbo a jika, idan Saraki ne ya yi nasara.
Atiku Abubakar da Peter Obi wanda ya yi masa takarar mataimaki a 2019, za su iya sake haɗewa kamar a 2019 ɗin, idan Atiku ne ya yi nasara.
Duk da Bala Mohammed Gwamnan Bauchi ya ce zai iya janye takarar sa idan tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya fito takara a APC ko PDP, hakan ba zai hana shi zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ba, idan wani da ya yi nasara a PDP ya yi tunanin ɗauko mataimaki na takarar PDP da Arewa maso Gabas.
Babu takamaiman wani hasashe kan ɗan takarar PDP Hayatuddeen. Amma dai ana abin ɗan takarar kamar tayar da ƙura ce kawai ya ke yi. Ko dai don hana ruwan wani gudu, ko kuma saboda neman wani abu na siyasa a gaba.
Rabi’u Kwankwaso na NNDP ba shi da wata alamar wanda zai tsayar takarar mataimaki. Amma dai ana ganin cewa zai ɗauko mataimaki ne daga Kudu maso Gabas.
Za ta iya kasancewa kuma ya dauki mataimaki daga ɗaya daga cikin ‘yan takarar APC, wanda ke ganin ba a yi masa adalci a zaɓen fidda gwani ba, idan ya fusata ya fice daga APC, ya bi Kwankwaso cikin NNDP, jam’iyya mai kayan marmari.