Ƙungiyar Jaddada Zaman Lafiya da Ci Gaban Najeriya (CNPD) ta gargaɗi APC cewa babu tsimi babu wata dabara, kawai idan dai ta na so ta ci zaɓe, to ta bai wa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 kawai.
Ƙungiyar ta shawarci APC ta yi amfani da tsohon shugaban ƙasar, wanda ta bayyana cewa shi ne “mafi cancanta” domin mulki ya koma a hannun sa a 2023.
A ranar Litinin ce CNPD ta yi wannan kiran a wurin wani taron manema labarai, a Abuja.
Wannan kiran ya zo ne kwanaki uku bayan da gungun wasu matasa suka iske Jonathan har gida, suka nemi ya fito takara.
Jonathan ya shaida masu cewa har yanzu dai bai yanke shawarar sake tsunduma cikin siyasa har ya nemi takara a ƙarƙashin APC ko wata jam’iyya ba.
Kiraye-kirayen da matasan su ka yi wa Jonathan ba ya da bambanci da na CNPD. Ƙungiyar ta shawarci a matsa wa Jonathan lamba ya amince ya tsaya takarar.
Babban Kodinetan CNPD mai suna Rapheal Okorie ya nuna damuwar sa ganin yadda Jonathan ke jan-ƙafa da ɓata lokacin tsunduma takarar shugabancin ƙasa ɗin.
“CNPD ba za ta sake shantakewa ta miƙe ƙafar ta zauna ba, har sai ta ɗauki matakan ganin ta tababar da ƙudirin ta na ganin Jonathan ya amince ya fito takarar ya tabbata.
An daɗe ana wannan raɗe-radin cewa Jonathan koma takara, kamar yadda Arewa ta tsara, domin ya sake karɓa, ya yi zango ɗaya, sannan mulki ya koma Arewa.
Da yawa na ganin cewa Jonathan zai yi ganganci da da-na-sani. Wasu kuma na ganin cewa idan ya shiga APC ɗin za yi nasara, bisa la’akari da cewa ɗimbin waɗanda Buhari ya bai wa muƙamai ‘yan PDP na lokacin Jonathan, da waɗanda suka canja sheƙa daga PDP zuwa APC suka yi nasara a gwamnoni, Sanatoci da Mambobin Tarayya duk su na nan danƙam cikin APC.
CNPD ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu su karɓi Jonathan hannu bibbiyu, su ba shi takara.