Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar kafa sabbin kwalejin kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin tarayya guda uku a faɗin kasar nan.
Kwalejojin sun haɗa da ɗaya a Kabo, jihar Kano, ɗaya a jihar Delta sai kuma na ukun a jihar Abia.
Kwalejon da aka kafa ta jihar Kano ya samo asali bayan sanata Barau Jibrin da ke wakiltar jihar a majalisa ya bayyana kudirin a yi haka a majalisar.
Bayan tattaunawa da majalisa tayi da bin sahu da sanatan ya rika yi hakan sa ya cimma ruwa.
Cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta fitar ranar Talata, tuni shugaban kasa ya rattaba hannu a kudirin kafa kwalejojin sannan kuma za su fara aiki a cikin watan sarumbar wannan shekara.
Kano na da jami’o’i da manyan makarantu mallakin gwamnatin Tarayya da gwamnatin jiha, amma dubannin dalibai basu samun gurbin karatu a duk shekara hakan yasa wasu ke cewa ana bukatar karin wasu.
Wannan yana daga cikin dalilan da yasa sanata Barau ya maida hankali sannan ya tabbatar bukatar kirkiro da wannan kwaleji ya tabbata.
Wasu da suka tattauna da wakilin mu a Kano gane da wannan kokari na sanata Barau, sun bayyana cewa suna alfahari da wakilcin sanatan.
” Muna alfahari da wakilcin sanata Barau a majalisar dattawa domin ba wannan kwaleji ba kawai gudunmawar da ya ke bada a wajen mahawara a majalisar abin farinciki ne ga duk wani ɗan yakin jihar Kano.” Inji Hassan Kasimu