Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya bayyana cewa an raba wa manoma miliyan 4.2 lamunin Naira biliyan 941.26 a ƙarƙashin shirin Bayar da Lamunin Bunƙasa Noma na CBN, wato ‘CBN Anchor Borrowers’.
Ya ce dukkan manoman miliyan 4.2 duk ƙananan manoma ne da ke noma kayan gona a faɗin jimillar hekta miliyan 5.4, inda su ke noma nau’ukan kayan gona iri 21 a faɗin ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa a kakar noma ta 2021, CBN ya raba lamunin Naira biliyan 193.59 ga manoma 923,699. Ya ce waɗannan manoma su na noma hekta miliyan 1.16.
Emefiele ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke jawabi Fadar Shugaban Ƙasa, yayin da Kwamitin Ƙungiyar Sarrafawa da Sayar da Takin Zamani ta kai wa Buhari ziyara.
A wurin ganawar, Shugaba Buhari ya ce Najeriya ta kusa zama ƙasar da babu kamar ta wajen wadatar takin zamani a Afrika.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ci gaban da ake samu wajen sarrafa sinadaran takin zamani ya kusa maida Najeriya ƙasa mafi bunƙasa wajen samar da taki a Afrika da duniya baki ɗaya.
Ya danganta wannan gagarimar nasara da irin “shirye-shirye masu tasiri” da gwamnatin sa ke bijiro da su a tsawon shekaru bakwai na mulkin sa.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaba Buhari, Femi Adesina ya fitar a ranar Talata, Shugaba Buhari ya yanzu da Najeriya ake gogayya a duniya wajen tseren samar da takin yuriya a duniya.
“Ganin yadda mu ke da sama da masana’antu 70 na sarrafa takin zamani a ƙasar nan, Najeriya ta kama hanyar zama ƙasar da ta tsere wa sauran ƙasashen Afrika wajen samar da takin zamani.
“Tabbas a yanzu Najeriya na sahun gaba a duniya wajen samar da yuriya.” Haka aka ruwaito Buhari ya bayyana a ganawar sa da Kwamitin Masu Sarrafawa da Sayar da Takin Zamani na Najeriya (FEPSAN), a ranar Talata, a Abuja.
Sanarwar ta ce Buhari ya ce wannan gagarimin ci gaba a cikin ƙanƙanin lokaci ya haifar da kwararar ɗimbin masu sha’awar zuba jari a fannin samar da yaƙin zamani.
Wannan kuwa a cewar sa, ya na samar da yalwa, albarka da albarka a cikin miliyoyin ‘yan Najeriya.
Shugaba Buhari ya nuna farin cikin sa don ganin cewa lokacin da ake kuka da ƙarancin takin zamani ya wuce, ya zama tarihi.
Daga nan ya jinjina wa FEPSAN saboda haɗa hannu da Gwamnati wajen nuna kishin bunƙasa harkokin noma a ƙasar nan.
“Lokacin da wannan gwamnati ta kama mulki cikin 2015, mun maida hankali wajen daƙile matsalar tsaro, bunƙasa tattalin arziki da kashe cin hanci da rashawa. Duk ƙasar da ke son ta ci gaba tilas sai ta inganta tattalin arzikin ta.” Inji Buhari.
“Nan da nan mu ka gano cewa babbar matsalar ƙarancin takin zamani ce babbar matsalar da manoman ƙasar nan ke fama da ita.”
“Shekarun da muka ɓata a baya can wajen fama da ƙarancin takin zamani, ya samo asali ne daga dogaron da muka yi wajen shigo da takin zamani daga wajen ƙasar nan. Sai gwamnatin mu ta ce tilas fa sai an canja wanzar tsari. Saboda Allah ya albarkaci Najeriya da dukkan sinadaran da ake bukata wajen samar da takin zamani.” Inji Buhari.
Ya buga misali da hatta a cikin yanayin korona ba a yi fama da ƙarancin takin zamani ba.
A jawabin sa, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya ce Najeriya za ta ci gaba da bayar da cikakken goyon baya wajen ganin a ki da yaushe takin zamani da harkokin noma sun bunƙasa a ƙasar nan.
Ya ce CBN ta raba sama da naira biliyan 114.09 wajen goyon bayan masana’antun samar da takin zamani a cikin shekaru biyar da suka gabata zuwa yau.