Zargi: Wani labari a facebook na zargin wai mutun na iya samun kwayoyin halittan da bas u da dangantaka da yaran shi saboda mutumin na da kwayoyin halitta biuy ko fiye
Yayin da mahawara dangane da gwajin kwayoyin halitta na DNA dan sanin ainihin iyayen yara ke daukar hankali, wani bincike na nuna cewa sakamakon gwajin na da sarkakiya domin wata sa’a sakamakon gwajin DNA kadai ba zai bayar da cikakken amsar da ake nema ba
Wata sa’a ba lallai ne gwajin DNA ya bayar da takamaiman amsa dangane da wadanda suka haifi yara ba, domin akwai wadansu abubuwa masu sarkakiya da kan taka muhimmiyar rawa.
Deoxyribonucleic acid wato DNA ko kuma kwayoyin halitta abubuwa ne da ‘yan adam da ma yawancin halittu ke gada daga wajen iyayensu. A kan yi amfani da shi wajen yin gwajin tantance mahaifin yaro ko yarinya, batun da ya zama babban abun tattaunawa a Najeriya bayan da aka sami karuwa a yawan mutanen da ke neman tantance iyayen yaransu na gaskiya.
Yayin da ake haka, masu amfani da shafin Facebook da dama sun yi zargin cewa yana iya yiwuwa sakamakon gwajin DNA ya nuna cewa uba ba shi da wata alaka da dansa ko ‘yar shi saboda mutun na iya samun kwayoyin halittar DNA biyu ko fiye. Dama dan adam na da kwayar halitta na DNA daya ne amma akwai wadanda suke da wanda ake kira Chimera a turance, wato wanda ke da kwayoyi biyu ko fiye. Dan haka, mai chimera zai iya haihuwan da da daya ta yadda sauran za su kasance ba su da wata alaka da dan.
Wata mai suna Princess Jessy-Doo ta yi wannan bayanin a shafinta na facebook, kadan daga cikin bayanin da ta yi y ace “Kwayar halittan dan adam na iya haihuwan yaran da ba su da alaka da shi tunda yana iya samun kwayoyi biyu ko fiye.”
Wata mai suna Lene Temitope ita ma ta bayyana yadda gwajin DNA ya kan kasance da sarkakiya, inda ta ce ya kamata a ce iyaye su yi gwaji su gani ko suna da Chimera kafin su yi gwajin na DNA.
Mutanen da suka yi tsokaci kan batun sun banbanta domin wadansu sun nuna rashin yadda wadansu kuma batun ya daure mu su kai.
Wani mai amfani da shafin na Facebook Aondofa Shedrack y ace ba zai yadda da wannan ba domin idan ba kwayoyin halittansa ba ne komai ba ne ke nan. Wani kuma mai suna Iji Silas ya yi godiya ne.
Shin wannan gaskiya ne? me ke sanya hakan, kuma yaya ya ke aiki? Wadannan tambayoyin ne su ka sa DUBAWA binciken wanann batun.
Tantancewa
Mun yi bincike sosai kan Chimerism wato kwayoyin halittan. Mun binciki yadda ya ke aiki kuma mun yi magana da kwararru a kan batun.
Mene ne Chimerism? Chemirism wani yanayi ne wanda jikin mutum zai kasance da kwayoyin halite biyu ko fiye. Wannan yanayin ba safai ake samu ba, ana hasashen mutane 100 ne kawai aka taba rubutawa a cikin mujallun masana kiwon lafiya. Wannan yanayi yana afkuwa a dabbobi ma.
Mutun ko dabba da ke da kwayoyin halittan da suka kai biyu ko fiye a kan kira shi Chimera.
Ire-Iren Chimera
Akwai Chimerism iri-iri kuma kowanne na da yadda ya ke bayyana. Akwai Microchimerism, artificial Chimerism, twin chimerism da tetregametic Chimerism.
Microchimerism – Wannan ya k n afku ne idan mace mai juna biyu ta dauki wasu kwayoyin halitta daga dan da take dauke da sh. A kan kuma sami akasin haka idan dan ne ya dauke kwayoyin halittan mahaifiyar.
Wadannan kwayoyin na iya shiga jinin uwa ko yaro su shiga gabobi daban-daban. Wadannan kwayoyin na iya tsayawa a cikin jikin dan ko uwar na tsawon shekaru 10 ko fiye.
Artificial Chimerism – Wannan kan afku ne idan aka yi wa mutun karin jinni, ko dashen kwayoyin halitta ko kuma dashen bargon kashi daga wani. Idan an yi haka kwayoyin halittan sai su shiga jikin mutun.
Yanzu, akwai magungunan da kan taimaka wajen karin jinni ko dashe ta yadda wanda ke samun jinin zai samu kwayoyin da ya ke bukata ba tare da sun manne ma jikin ba.
Twin Chimerism – Wannan shi ne matsanancin wanda kuma aka fi magana a kai a Najeriya. Irin wannan kan faru ne idan mace ta yi cikin tagwaye sai daya ya rasu a ciki ya bar daya, sai wanda ya rayun ya dauki wasu daga cikin kwayoyin halittan wanda bai yi rai ba. Wannan ne zai baiwa wanda ya rayun kwayoyin halitta biyu.
Tetragametic Chimerism – Wannan yakan afku ne idan kwan na miji ya hadu da kwayayen namace guda biyu wadanda suka hadu suka zama daya.
Yadda Chimerism ke bayyana
Alamun chimerism kan banbanta daga mutun zuwa mutun kuma da yawa wadanda ke da wannan yanayin ma ba suwa nuna alamu kuma ma bas u fahimtar alamun k da sun bayyana.
Wadannan alamun sun hada da:
• Duhu a fatan jiki ko kuma haske, wata sa’a a wurare kadan wata sa’a kuma da yawa.
• Launin idanu daban-daban
• Wata sa’a ba’a gane ko wanda aka haifa namiji ne ko namace.
• Kwayoyin halittan DNA iri biyu
• Yiwuwar samun cututtukan da ke shafan garkuwan jikin mutun ko kuma kwakwalwa.
Mun gano wadansu wadanda suke da matsalolin da ke da nasaba da Vhimerism. Wadnasunsu sun hada da mawakin Carllifornia Taylor Muhl, wani dan asalin Amurka, da wata mata mai suna Lydia Fairchild da ke zaune a Washington. Wadannan sun nuna irin yadda chimerism ke bayyana.
Ra’ayoyin Kwararru
Dr Okpanachi Achile wani ma’aikacin lafiya da ke asibitin kwararru na Rehoboth a Lokoja ya yi bayanai da yawa dangane Chimerism kama daga wanda ya shafi dashen bargo zuwa cikin tagwayen da a kan rasa guda.
Ya bayyana cewa a yanayin da ya shafi tagwayen da daya kan bata ya bar daya, wanda ya rayu yawancin lokuta ya kan shanye wanda bai yi rai ba ta yadda ko an dub aba za’a gan shi ba. Wannan ne ke kai ga samun DNA iri biyu domin dama can kowannensu na da na shi.
“Gabobin da ya shanye ne ke janyo DNA kala biyu wadanda su kan kai ga abin da ake kira Chimera cin. Haka nan kuma idan aka yid ashen bargo, nan ma ana iya samun Chimera” a cewar Okpanachi.
Wani likitan mata da Asibitin Kasa a Najeriya wato Natinal Hospital Dr. Jeremiah Agim ya ce wannan tsohon labari ne kuma abin na iya kasasncewa kalubale idan ha rana bukatar tantance mahaifin mutun.
A Karshe
Binciken mu da kwararrun da muka yi magana da su sun bayyana mana cewa mutane na iya samun DNA biyu kuma suna iya haifan yaran da basu da wata alaka da su a fanin DNA. Wani yanayi ma suna Chemirsm a turance ke janyi hakan. Dan haka wannan zargin gaskiya ne